Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-01 18:59:03    
Yin yawon shakatawa a jihar Tibet, inda aka dandana abinci mai dadin ci

cri

Mutane su kan mayar da cin abinci a gaba da kome. Sa'an nan kuma, abinci irin na kasar Sin ya kasance abun sha'awa ga mutane a duk duniya. Wasu na ganin cewa, a yayin da kasar Sin ta zama masana'anta ta duniya, to, a sa'i daya kuma, kasar Sin tana kasancewa a matsayin dakin dafa abinci na duniya. Wannan ya kawo wa jama'ar Sin alheri, haka kuma, shi ne alherin da kasar Sin take kawo wa mutanen duk duniya.

Abinci irin na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin, wani kyakkyawan misali ne na abinci irin na kasar Sin. Jihar Tibet tana tudu a kudu maso yammacin kasar Sin, fadinta ya yi girma, amma babu mutane da yawa da ke zama a wurin. Saboda dalilan muhallin halittu da wurin da take kasancewa da kuma karfinta wajen samar da abinci, shi ya sa jihar Tibet ba ta iya sayar da dimbin abincin da take samarwa zuwa ketare ba, ta fi sayar da abincinta a gida. Dukkan masu saye-saye na gida da kuma na waje sun nuna babban yabo kan abinci irin na jihar Tibet mai dadin ci.

Bisa kididdigar da aka samu, an ce, a matsayin wani wuri a kasar Sin da masu yawon shakatawa suka fi son kawo masa ziyara, jihar Tibet ta fi jawo hankulan masu yawon shakatawa daga kasashen Amurka da Japan da Turai. A kwanan baya, a karo na farko ne yawan masu yawon shakatawa na Japan da suka kawo wa jihar Tibet ziyara ya wuce na Amurka, ta haka Japan ta zama ta farko a duniya. Yawan kudaden da masu yawon shakatawa na ketare suka kashe domin cin abinci a jihar Tibet ya kai sulusin jimlar kudaden da suka kashe domin yin yawon shakatawa a wurin.

Ko da yake mutanen Japan da na kasashen yammacin duniya suna kallon abincin da kasar Sin take samarwa da tunaninsu, amma su kan ci albarkatun bakinsu a jihar Tibet. Dalilin da ya sa hakan shi ne domin abinci irin na kasar Sin na da matukar dadin ci. Abinci irin na kasar Sin na iya bayyana ainihin abinci, kasar Sin kuma aljanna ce ta cin abinci. Saboda jihar Tibet na kan tudun da ke da kankara, shi ya sa abinci irin na Tibet na da inganci sosai, kuma suna kunshe da abubuwa masu gina jiki masu tarin yawa. Jihar Tibet tana kan tudun, ana karancin iskar oxygen. Babu manyan masana'antu da suke gurbata muhalli a jihar Tibet, an dade ana rana a wajen. Dukkan danyun abubuwan da aka yi amfani da su wajen dafa abinci sun girma ne a cikin kyakkyawan muhalli. Kazalika kuma, ana sarrafa abinci bisa tsattauran ma'aunin da aka tsara.

Bugu da kari kuma, dukkan abinci irin na jihar Tibet ana samar da su da sarrafa su da kuma sayar da su a karkashin sa ido da gwamnatin Sin take yi a tsanake. Mun yi imani da cewa, nan gaba ba da dadewa ba, a kasuwannin kasa da kasa, abinci irin na jihar Tibet zai sami karbuwa sosai kamar yadda suke yi a kasuwar gida.