Yau wato ran 1 ga watan Afril, jaridar Global Time ta kasar Sin ta buga sharhin cewa, gungun mutane mabiya Dalai Lama na neman sanya batun Tibet cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing.
Sharhin ya bayyana cewa, a kwanan nan, Dalai Lama ya yi karya ga duk duniya kan cewa, wai tun farko yana goyon bayan damar da aka bai wa kasar Sin wajen shirya gasar wasannin Olympics, har yanzu yana tsayawa tsayin daka kan wannan matsayi. Amma tun tuni yunkurin Dalai Lama na sanya batun Tibet cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing ba abu ne na asiri ba. Ya zuwa yanzu ana iya samun labarun da gungun mutane mabiya Dalai Lama suka bayar a tashar Internet tasu don zuga wasu kasashe da su sanya batun Tibet cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing lokacin da suke tuntubar kasar Sin.
Haka kuma sharhin ya ce, zuga mutane da su yi adawa da gasar wasannin Olympics ta Beijing ba zai samu amincewa daga duniya ba. Burin gungun mutane mabiya Dalai Lama shi ne neman sanyan batun Tibet cikin gasar wasannin Olympics ta Beijing ta hanyar tada ala'muran tashe-tashen hankali, amma ba ya son amincewa da wannan a fili.(Kande Gao)
|