Yau 1 ga wata da safe, da misalin karfe 10, agogon birnin Beijing, jirgin saman da ke dauke da wutar wasannin Olympics ta Beijing ya tashi daga filin jirgin sama na birnin Beijing, zuwa birnin Alma-ata, birni mafi girma a kasar Khazakstan, wanda ya kasance zango na farko a kan hanyar mika wutar wasannin Olympics ta Beijing a kasashen waje. Wannan kuma ya nuna cewa, an fara mika wutar wasannin Olympics a kasashen waje.
Kungiyar kula da mika wutar wasannin Olympics da ke karkashin jagorancin Mr.Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin kula da wasannin Olympics na birnin Beijing, za ta bi wutar don ba da kariya ga aikin mika wutar a kasashen waje.
An ce, za a shafe tsawon kwanaki 130 ana mika wutar wasannin Olympics, kuma tsawon hanyar ya kai kilomita dubu 137, a yayin da masu mika wutar za su wuce dubu 21. Sabo da haka, mika wutar wasannin Olympics a wannan karo zai zo na farko wajen tsawon lokaci da yawan masu mika wutar a tarihin wasannin Olympics. (Lubabatu)
|