Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-31 20:17:19    
An samu ra'ayi daya kan batun Taiwan a tsakanin Sin da Japan

cri
A ran 31 ga wata, janar Ma Xiaotian, mataimakin babban hafsan hafsoshin sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ya yi shawarwari a karo na 8 da masuba Kohe, mataimakin ministan tsaron kasar Japan a nan birnin Beijing kan batun tsaron da tabbatar da kwanciyar hankali a tsakanin kasashen biyu, inda suka samu ra'ayoyin bai daya a batutuwa iri daban-daban, ciki har da batun Taiwan da batun yin musayar harkokin tsaro.

Bayan shawarwarin, janar Ma Xiaotian ya gaya wa manema labaru cewa, a kan batun Taiwan, ya bayyana wa bangaren kasar Japan matsayin da kasar Sin ke ciki da manufofin da kasar Sin ke dauka, kuma ya bayyana musu abubuwan da ke jawo hankulan bangaren kasar Sin kan batun. Sabo da haka, Masuba Kohe ya yi bayani daya bayan daya ne kan abubuwan da ke jawo hankulan bangaren kasar Sin. Ya kuma jaddada cewa, gwamnatin kasar Japan tana tsayawa tsayin daka kan matsayinta kan batu Taiwan. Bangaren kasar Japan bai canja alkawuran da ya dauka a cikin takardun siyasa, ciki har da Hadaddiyar Sanarwar da aka kulla a tsakanin kasashen Sin da Japan.

Game da batun yin musaye-musaye da hadin kai kan harkokin tsaron kai a tsakanin kasashen biyu, bangarorin biyu sun samu ra'ayoyi bai daya kan jerin matakai, ciki har da kai wa juna ziyara a tsakanin manyan shugabannin kasashen biyu, kuma a tsakanin hafsoshi matasa. (Sanusi Chen)