
A ran 31 ga wata, wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008, wadda aka same ta a birnin Olympia, ta iso nan birnin Beijing. A ran nan da safe, kasar Sin ta shirya bikin maraba da wutar gasar wasannin Olympics ta Beijing da kaddamar da mika wutar yola a filin Tian'anmen.
Shugaban kasar Sin Mr Hu Jintao ya halarci bikin, haka kuma ya mika wutar yola ta farko ga shahararren 'dan wasa na kasar Sin Mr Liu Xiang, wanda yake kiyaye matsayin farko na gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110. Sa'an nan kuma, Mr Hu ya sanar da kaddamar da bikin mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008.

Mataimakin shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya bayar da wani jawabi a gun bikin cewa, shirya gasar wasannin Olympics da ke da abubuwan musamman bisa babban matsayi, ya zama buri daya na dukkan jama'ar kasar Sin.
Shugaban kwamitin daidaita harkokin gasar wasannin Olympics ta Beijing daga hukumar gasar wasannin Olympics ta duniya wato Mr Hein Verbruggen ya karanta wasikar fatan alheri da shugaban hukumar gasar wasannin Olympics ta duniya Mr Jacques Rogge ya rubuta cewa, lokacin shirya gasar wasannin Olympics ta Beijing ba ma kawai lokaci ne da za a samun nasarorin wasanni ba, har ma ya zama wata kyakkyawar dama da jama'ar kasar Sin da jama'ar duk duniya za su koyi juna da fahimci juna, da girmamawa juna.(Danladi)
|