Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-31 16:51:16    
Wasu jami'an diplomasiyya na kasashen duniya da ke nan kasar Sin sun goyi bayan matakan da gwamnatin Sin ta dauka kan batun Tibet

cri
A ran 28 ga watan Maris, wasu jami'an diplomasiyya na kasashen waje da ke nan kasar Sin sun kai ziyara ta kwanaki 2 a birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai cin gashin kanta domin gano matsalar barkewar mummunan tashin hankali a ran 14 ga watan Maris. Bayan da suka ganewa idanunsu mummunar asarar da aka samu sakamakon wannan tashin hankali, jami'an diplomasiyya sun bayyana cewa sun fahimta kuma sun nuna goyon baya ga matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan wannan matsala.

Wadannan jami'an diplomasiyya sun zo ne daga ofisoshin jakadancin kasashen Brazil da Amurka da Britaniya da Singapore da Tanzania da Rasha da suke nan kasar Sin. Da isarsu a birnin Lhasa, da farko dai sun je wani kantin sayar da tufafi mai suna "Yi Chun" da aka kone shi gaba daya, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan mata 5 wadanda suke aiki a wannan kanti. 'Yan diplomasiyya sun yi mamaki kuma sun ji bacin rai ga abubuwan da suka gani. Mr. George Manongi, karamin jakadan kasar Tanzania da ke nan kasar Sin ya ce, "Idan ba mu zo nan ba, ba za mu iya fahimtar hakikanan abubuwa ba. Muna farin ciki domin gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai wajen kwantar da kura."

Madam Foo Teow Lee, karamar jakadan kasar Singapore da ke nan kasar Sin ta bayyana cewa, "Ina tsammani cewa, tabbas ne gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan da suka wajaba kan irin wannan matsalar nuna karfin tuwo domin tsaron lafiyar jama'ar Lhasa. Muna goyon bayan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka." (Sanusi Chen)