Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-31 16:46:05    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya, wakilinmu ya samu labari daga wajen hukumar sufuri ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, a shekarar da muke ciki, jihar Tibet za ta ware kudin Sin Yuan biliyan 6 domin shimfida hanyoyin mota, ta yadda za a yi kokarin tabbatar da gundumomi da garuruwa da yawansu ya kai kashi 99 cikin 100 bisa na duk jihar Tibet za su samu hanyoyin mota.

An ce, jimlar tsawon hanyoyin mota da aka samu yanzu a duk jihar Tibet ya kai kilomita dubu 44.8, kuma an kiyasta cewa zuwa shekarar 2010, wannan adadi zai kai kilomita dubu 50. Manoma da makiyaya na jihar Tibet suna ta kara samun kudin shiga da yawa ta hanyar shiga ayyukan shimfida hanyoyin mota, sa'an nan kuma za su iya yin jigilar amfanin gona da na dabbobi da sauri ta hanyoyin mota. Ban da wannan kuma bisa karuwar yawan hanyoyin mota da aka shimfida a kowace rana, yawan kudin shiga da manoma da makiyaya na jihar Tibet za su samu shi ma zai karu daga wajen sana'ar yawon shakatawa.

---- Mr. Wang Lequan Sakataren kwamitin jam'iyyar kwaminis ta Sin na jihar Xinjiang ta kabilar Uighur mai ikon tafiyar da harkokin kanta ya furta kwanan baya a nan birnin Beijing cewa, jihar Xinjiang ta riga ta zama muhimmin sansanin samar da man fetur da gas na kasar Sin.

Wang Lequan ya ce, yawan man fetur na jihar Xinjiang ya dauki kashi 30 cikin dari bisa na duk kasar, kuma yawan gas ya dauki kashi 34 ciki dari bisa na duk kasar. Sabo da dalilai da dama, ba a yi amfani da makamashin jihar Xinjiang sosai ba, amma an yi imani da cewa, domin ana kokarin nazarin yin amfani da su yanzu, jihar Xinjiang za ta kara daukar nauyin samar da makamashi a nan gaba.

Bugu da kari, Wang Lequan ya nuna cewa, jihar Xinjiang tana da albarkatun kwal sosai, a nan gaba, jihar za ta raya masana'antun samar da wutar lantarki ta hanyar yin amfani da kwal don samar wa sauran larduna da birane wutar lantarki, a sa'i daya kuma, za ta kara bunkasa masana'antun sarrafa magunguna ta hanyar yin amfani da kwal.