Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-31 16:42:23    
Saurayi Mugodo Joseph, dan kasar Zimbabwe da kantinsa na sayar da kayayyakin tsaraba a kasar Sin

cri

A birnin Taiyuan na lardin Shanxi da ke a rewacin kasar Sin, saurayi Mugodo Joseph, dan kasar Zimbabwe yana gudanar da wani kantin sayar da kayayyakin tsaraba kamar saiwayoyin itatuwa da katako da aka sassaka da kuma lu'ulu'u da sauransu wadanda aka kawo su daga nahiyar Afrika da ta Asiya da kuma Turai. An ce, kantinsa kanti ne na farko da baki 'yan kasashen ketare suka kafa a lardin Shanxi. Yayin da wakilin gidan rediyonmu ya shiga cikin kantin don kai ziyara, sai Mugodo Joseph ya tarye shi da hannu bibbiyu, sa'an nan ya yi magana cikin Sinanci cewa, "Sannu da zuwan karamin kanti na Mugodo Joseph"

Mugodo Joseph, barbarar 'yanyawa ne. Mahaifinsa dan kasar Zimbabewe wani makaniken jirgin sama ne, mahaifiyarsa kuma 'yar kasar Birtaniya wata malamar koyarwa ce. Mugodo Joseph ya kafa kantinsa a watan Satumba na shekarar bara. Ko da yake kantinsa ba shi da fadi, amma yana sayar da kayayyakin tsaraba iri daban daban.

Mugodo Joseph ya gaya wa wakilinmu cewa, kafin zuwansa a kasar Sin, ya taba yin yawon shakatawa a kasashe daban daban. A dukkan wuraren da ya sa kafa, ya kan sayi wasu kayayyakin tsaraba wadanda ke da sigar musamman na wurin don tattara su. Da ya sami kayayyakin tsarabar masu dimbin yawa, sai ya shiga cikin tunanin bude wani kantin sayar da su. Bayan zuwansa a kasar Sin, ya zama wani malamin da ke koyar da Ingilishi a Kolejin Koyon Aikin Masana'antu Da Kasuwanci na lardin Shanxi. Da ya tabo magana a kan makasudin kafa kantinsa, sai ya bayyana cewa, "makasudin kafa kantina shi ne domin nuna wa mutane cewa, ana iya samun kayayyakin tsaraba na wurare daban daban na duniya a lardin Shanxi na kasar Sin. Sa'an nan na iya yi wa aminan kasashen waje farfaganda a kan kasar Sin. Haka kuma Sinawa na wurin su ma za su fahimci cewa, muna zama tare da duk mutane cikin daidaici, muna nuna musu aminci daidai kamar yadda babban taken wasannin Olympic dinmu wato "duniyarmu daya, burinmu ma daya".

Da Mugodo Joseph ya tabo magana a kan wasannin Olympic na Beijing, sai ya ce, don cim ma babban taken wasannin Olympic na Beijing wato "duniyarmu daya, burinmu ma daya", ya taba shiga takarar zaman wani mai aikin sa kai na wasannin Olympic a kwanakin baya. Dukkan baki na kasashen waje da suka shiga cikin takarar sun wuce 500. Ko da yake ya zama daya daga cikin dari da suka ci nasara a mataki na farko, amma bai zama daya daga cikin masu cin takara 8 daga karshe ba. Mugodo Joseph ya ce, yana fatan nan gaba zai sami damar zama daya daga cikin masu aikin sa kai na wasannin Olympci na Beijing daga karshe. Kuma yana son kafa kantinsa na biyu da na uku da na hudu a sauran birane na kasar Sin, zai iya auren wata budurwar lardin Shanxi. Malama Li Yufeng, aminiyar Mugodo Joseph ta bayyana a kan wannan cewa, "a cikin zuciyata, Mugodo Joseph wani mutum ne mai babban buri da kishin takara. A cikin wani tsawon lokaci, ya yi ta yin kokari ba tare da kasala ba, kuma ya yi aikin wurjanjan. Dukkan mutanen wurinmu muna yi masa fatan alheri, muna fatan zai kara jin dadin zamansa a nan kasar Sin. Sa'an nan bisa kokarin da yake yi, zai kara cimma burinsa sannu a hankali, zai kara gamsar da zamansa. Da zuciya daya muna yi masa fatan alheri." (Halilu)