Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-31 15:16:07    
Li Changchun ya yi shawarwari tare da babban sakataren jam'iyyar CDR ta Tunisiya

cri

A ranar 29 ga wata da yamma, agogon kasar Tunisia, zaunannen wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin, Mr.Li Changchun, wanda a halin yanzu ke yin ziyarar aiki a kasar Tunisia, ya yi shawarwari tare da Hedi M'henni, babban sakataren Constitutional Democratic Rally, ko jam'iyyar dimokuradiyya ta tsarin kasar Tunisia, wato jam'iyyar da ke rike da ragamar mulkin kasar Tunisia.

A lokacin shawarwarinsu, Mr.Li Changchun tare kuma da Mr.Hedi M'henni sun yi musanyar ra'ayoyi a kan al'amuran duniya da na shiyya shiyya wadanda ke daukar hankulansu gaba daya. Li Changchun ya ce, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Tunisia, kasashen biyu sun yi ta kara amincewa da juna a fannin siyasa, kuma hadin gwiwar da ke tsakaninsu da fannonin tattalin arziki da ciniki ya yi ta habaka, sa'an nan, hadin gwiwar da ke tsakaninsu a kan harkokin duniya da na shiyya shiyya ya yi ta inganta, ya ce,"A cikin shekarun baya, huldar siyasa da ke tsakanin kasashenmu biyu ta kara bunkasa, kuma mun kara amincewa da juna a fannin siyasa. Bayan haka, muna daukar matsayi daya ko kusan daya a kan yawancin manyan al'amuran duniya, kuma a cikin harkokin duniya, muna hadin gwiwa da juna yadda ya kamata, don kiyaye moriyar kasashe masu tasowa. A fannin tattalin arziki kuma, cinikin da ke tsakaninmu ya karu sosai, a yayin da hadin gwiwarmu ya yi ta bunkasa a fannonin sadarwa da kayayyakin gida da ke aiki da lantarki da fasahohin zamani da yawon shakatawa da al'adu da ilmi da dai sauransu."

Mr.Li Changchun ya ce, Sin za ta yi kokarin tabbatar da matakai guda takwas da shugaba Hu Jintao na kasar ya gabatar, kuma tana son inganta hadin gwiwar cin moriyar juna a tsakanin kasashen biyu, don kara kawo wa jama'arsu alheri. Ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, da Sin da Tunisia na daukar nauyi daya, wato kiyaye kwanciyar hankalin al'umma da bunkasa tattalin arzikinsu da kawo wa jama'a alheri. Sabo da haka, gaggauta bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu ya dace da moriyar jama'arsu, haka kuma zai amfana wa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashe masu tasowa da zaman lafiyar duniya. A matsayinsu na jam'iyyun da ke rike da ragamar mulkin kasashen biyu, tabbatar da kyakkyawar hulda a tsakanin jam'iyyar kwaminis ta Sin da jam'iyyar dimokuradiyya ta tsarin kasar Tunisia na da muhimmanci sosai wajen inganta amincewa da juna a fannin siyasa da kara sa kaimi ga hadin gwiwar da ke tsakaninsu a fannoni daban daban. Sabo da haka, Mr.Li Changchun ya gabatar da shawarwari 3 game da inganta mu'amala a tsakanin jam'iyyun biyu. Ya ce,"a shekara mai zuwa, za a cika shekaru 30 da kulla hulda a tsakanin jam'iyyun biyu, kuma na shawarci a ci gaba da tabbatar da ziyarar juna a tsakanin tawagogin manyan wakilan jam'iyyun biyu, don su kara amincewa da juna a fannin siyasa, ta yadda za a ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen biyu gaba daga dukan fannoni. Na biyu, a tabbatar da cudanya da juna a tsakanin jam'iyyun biyu a fannoni daban daban kuma ta hanyoyi iri iri. Na uku, a yi amfani da mu'amalar da ke tsakanin jam'iyyun biyu, don kara nema wa jama'ar kasashen biyu alheri, da bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban."

Daga nasa bangaren kuma, Me.Hedi M'henni ya ce, Tunisia na son kokarin bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu, ta yadda huldar za ta kasance wani kyakkyawan misali ta fuskar mu'amalar jam'iyyu da na kasa da kasa. Ya kuma sake jaddada cewa, Tunisia na nuna tsayayyen goyon baya ga kokarin da Sin ke yi wajen kiyaye cikakken yankinta da mulkin kanta, ya ce"Bangarorinmu biyu na dukufa kan tabbatar da zaman lafiya da bunkasa mulkin kan kasashe daban daban da girmama shi. Kullum Tunisia na nacewa ga bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana nuna goyon baya ga mulkin kan kasar Sin a kan yankunanta gaba daya. Ma iya cewa, huldar da ke tsakanin kasashenmu biyu wani kyakkyawan misali ne a fannin huldar da ke tsakanin kasa da kasa."(Lubabatu)