Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-30 20:29:19    
Rukunin Dalai Lama shi ne ya shirya da zuga al'amuran aikata laifuffuka da aka tayar a birnin Lhasa

cri
A ran 30 ga wata, kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya bayar da wani bayanin, cewa rukunin Dalai Lama shi ne ya shirya da kuma zuga al'amuran aikata laifuffuka da aka tayar a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin.

Bayanin ya nuna cewa, bayan da rukunin Dalai Lama ya gudu domin cin tura a cikin boren da ya tayar a shekara ta 1959, har kullum yana neman kawo wa kasar Sin baraka. Bayan da birnin Beijing ya cimma nasara wajen samun iznin shirya gasar wasannin Olympics ta shekara ta 2008, rukunin Dalai Lama ya fitar da kirari na wai yaki da wasannin Olympics domin neman kawo cikas ga gasar wasannin Olympics da kuma sa kaimi ga yunkurin neman 'yancin kan Tibet. Ban da kuma ya gudanar da jerin al'amura a gida da waje domin lalata gasar wasannin Olympics ta Beijing.

Kuma bayanin ya ce, a ran 14 ga wata, rukunin Dalai Lama ya zuga wasu masu tarzoma da su aikata manyan laifuffuka a birnin Lhasa. A ran nan kuma, rukunin ya kira taro, inda ya tsai da kudurin cewa, ma'aikatar kudi ta gwamnatin gudun hijira ta Tibet ta kula da aikin tattara kudade domin goyon bayan rukunin a fannin kudade don yaki da gwamnatin kasar Sin. A waje daya kuma, a karkashin jagorancin rukunin Dalai Lama, an kai farmaki ga ofishoshin jakadun kasar Sin fiye da 10 da ke kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da Indiya da dai sauransu.(Kande Gao)