Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-30 16:57:05    
Kamfanin dillancin labaru na Xin Hua ya bayar da sharhi kan maganar Hans Gert Poettering game da batun Tibet

cri
A ran 30 ga wata, kamfanin dillancin labaru na Xin Hua, wato wani kamfanin dillancin labaru mafi girma a nan kasar Sin ya bayar da wani sharhi mai lakabi haka "daina yin hayaniya ba tare da daukar hakki ba". A cikin wannan sharhi, an ce, a kwanan baya, Mr. Hans-Gert Poettering, shugaban majalisar dokokin kungiyar tarayyar Turai ya yi wasu maganganu ba tare da daukar hakki ba kan matsalar nuna karfin tuwo da aka yi a wasu wuraren jihar Tibet, ciki har da birnin Lhasa, maganganu ne da ke tayar da baki fari, kuma ya yi irin wadannan maganganu ne ba tare da daukar hakki ba.

Wannan sharhi ya ce, matsalar Lhasa matakin nuna karfin tuwo ne da rukunin Dalai Lama ya mai da hankali sosai wajen shiryawa da tayar da shi sosai da sosai domin yunkurin kawo wa kasar Sin baraka. Matakan dukewa da kone-kone da kwacewa da tsirarrun mutane suka yi sun keta hakkin dan Adam, kuma sun lalata kwanciyar hankali da odar doka ta zaman al'umma. Gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai bisa doka domin tabbatar da kawnciyar hankali a birnin Lhasa da sauran wuraren kasar wajababbun matakai ne na daidai da suka samu fahimta da goyon baya daga kasashe fiye da 100 na duk duniya.

Wannan sharhi ya kuma ce, maganganun da Poettering ya yi sun bayyana cewa, har yanzu wasu mutanen yammacin duniya suna nuna bambancin siyasa. Irin wadannann maganganun ba za su samu amincewa ba a duk duniya, kuma suna lalata ran jama'a fiye da biliyan 1.3. (Sanusi Chen)