Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-30 16:39:08    
Gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta tallafa wa yankin Tibet domin neman cigaban tattalin arziki da zaman al'umma

cri
Bisa sabuwar kididdigar da aka yi, an ce, a shekara ta 2007, jimlar kudaden da aka samu a jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin ta kai kudin Sin yuan biliyan 34.2, matsakaicin yawan kudin GDP ya kai fiye da kudin Sin yuan dubu 12, wato tattalin arzikin jihar Tibet ya karu da kashi 12 cikin kashi dari a kowace shekara cikin shekaru 7 da suka gabata.

A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, gwamnatin tsakiya ta Tibet ta kara karfin tallafawa jihar Tibet. A shekarar 2006, majalisar gudanarwa, wato gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta bayar da manufofi masu gatanci 40 domin neman cigaban Tibet da tabbatar da kwanciyar hankali a jihar. A shekarar 2007, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kuma tabbatar da muhimman ayyukai 180 da za a zuba kudin Sin yuan fiye da biliyan 77 a cikinsu.

Gwamnatin jihar Tibet ta bayyana cewa, bisa shirin da ta tsara, za ta kebe kudin Sin yuan fiye da biliyan 20 domin tabbatar da raya muhimman ayyukai 77 a shekarar da muke ciki. (Sanusi Chen)