Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-29 17:41:43    
Hukumar jihar Tibet ta Sin ta ba da kudaden diyyar mamata ga iyalan mutanen da suka rasa rayukanku a tarzomar Lhasa

cri
Jiya Jumma'a, hukumar jihar Tibet mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kasar Sin ta sanar da cewa, ta tsaida kuduri kan ba da kudaden diyyar mamata ga iyalan mutane 18 wadanda ba su ci ba su sha ba suka rasa rayukansu a cikin tashin hankalin da ya auku a birnin Lhasa a ran 14 ga wata. Yawan kudin da aka bai wa ko wane mutum da ya rasa rai ya kai kudin Sin Yun dubu 200.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin jihar Tibet za ta yi binciken matakan da za ta dauka don ba da agaji ga jama'a da ba su ci ba su sha ba suka ji raunuka a cikin tarzomar da aka tayar ta kai farmaki kan jama da farfasa kayayyaki da wawashe su da sa wurare wuta a ran 14 ga wata a birnin Lhasa, da kuma ba da agaji ga sake gina kantuna da gidajen jama'a da aka lalata su a cikin tarzomar.

A kwanan baya, Mr Lobsang Daindzin, mataimakin shugaban jihar Tibet ya bayyana cewa, yanzu an riga an sami nasarar farko wajen daidaita lamarin da ya auku a birnin Lhasa a ran 14 ga wata. Ko kusa Dalai Lama ba zai cim ma makarshiyarsa ta neman balle jihar Tibet daga kasar Sin ba har abada. Haka kuma dukkan makarkashiyar da aka kulla don neman lalata zaman lafiya da jituwa da ci gaba a Tibet ba ta sami goyon baya daga wajen jama'a ba, kuma tabbas ne za ta bi ruwa.

Mr Lobsang Daindzin, ya kara da cewa, Dalai Lama ya kira da a hada "batun Tibet" da wasannin Olympic na Beijing a gun daya, don neman cim ma makarkashiyar siyasarsa ta lalata wasannin Olympic na Beijing. A lokacin da za a ba da wutar wasannin Olympic a jihar Tibet da dutsen Everest, jama'ar jihar Tibet tana cike da imani, kuma ta kware sosai wajen hana rukunin Dalai Lama ta da zaune tsaye, za ta kammala aiki mai girma da Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da kasar Sin suka danka mata. (Halilu)