Mataimakin shugaban jihar Tibet da ke da ikon tafiyar da harkokinta da kanta Mr Padma Tsinle ya bayyana cewa, a halin yanzu dai, an riga an tsare mutane 414 bisa laifuffukan fasa wurare da kwashe kayayyakin jama'a a ran 14 ga wata a birnin Lhasa.
Mr Padma Tsinle ya ce, bisa doka, an riga an tsare mutane 414, bisa binciken da aka yi, hukumar bin bahasin ta birnin Lhasa ta kama mutane 30 daga cikinsu, haka kuma mutane 53 sun gudu a waje.(Danladi)
|