Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 16:42:34    
Hukumar Lhasa ta amince da cafke mutane 30 da ake tuhumarsu da aikata laifuffukan fasa wurare da kwashe kayayyaki

cri
Yayin da mataimakin shugaban din-din-din na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin Padma Tsinle ke zantawa da manema labaru na ketare jiya 27 ga wata, ya bayyana cewar, ya zuwa yanzu, hukumar gabatar da kararraki ta Lhasa ta riga ta amince da cafke mutane 30 wadanda ake tuhumarsu da aikata munanan laifuffuka na fasa wurare, da kwashe kayayyaki, tare kuma da cunnawa wurare da dukiyoyi wuta a ranar 14 ga watan da muke ciki a Lhasa.

Bisa labarin da aka samu, an ce, an tuhumi wadannan mutane ne da munanan laifuffukan kawo babbar illa ga tsaron kasa, da fasa wurare, da kwashe kayayyaki, da kuma cunnawa wurare da dukiyoyi wuta. Haka kuma, akwai kwararan shaidu wadanda suka shaida laifuffukansu.

Mr. Padma Tsinle ya ce, a halin yanzu, yawan mutanen da ake tsare da su bisa doka ya kai 414, akasarinsu'yan kabilar Tibet ne, amma akwai 'yan kabilar Han. Zuwa yanzu, akwai mutane kusan 300 wadanda suka kai kansu ga ofishin 'yan sanda, kuma an riga an saki 111 daga cikinsu.(Murtala)