Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 16:39:59    
Ana aiwatar da manufar bin addinai cikin 'yanci daga dukkan fannoni a Tibet

cri
Yayin da mataimakin shugaban babbar kolejin koyon addinin Buddah ta tsarin harshen Tibet na kasar Sin Nagtsang Champa Ngawang ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewar, ana aiwatar da manufar bin addinai cikin 'yanci daga dukkan fannoni a jihar Tibet.

Mr. Nagtsang ya ce, mabiya addini sun kara samun arziki da ababen hawa masu kawo sauki wajen tafiyar da harkokin addininsu, biyo bayan bunkasuwar zaman rayuwar jama'ar jihar Tibet mai cin gashin kanta. Yayin da hukumar wurin ke matukar kokarin marawa Tibet baya wajen raya tattalin arzikinta, tana mutunta harshe, da al'adu, da yanayin rayuwa da al'ada, da addinai daban-daban na wurin. A halin yanzu, ana aiwatar da manufar bin addini cikin 'yanci daga dukkan fannoni yadda ya kamata a Tibet.

Mr. Nagtsang ya kara da cewar, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kebe makudan kudade domin sabuntawa da kare wuraren ibada na Tibet, da sa ido da kiyaye littattafan addinin Buddah masu daukaka na kabilar Tibet, da kulawa zaman rayuwar mabiya addinin Buddah, tare kuma da kafa tsarin bada tabbaci ga zaman rayuwarsu.(Murtala)