Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 14:21:36    
An kammala aikin share fage ga zabubukan hadin gwiwa na kasar Zimbabwe

cri
A ran 29 ga wata, za a shirya zabubukan shugaba da 'yan majalisar dokoki da kuma gwamnatocin wurare daban daban a kasar Zimbabwe da ke kudancin Afirka. Yanzu an riga an kammala dukkan ayyukan share fage ga zabubukan hadin gwiwa.

Gwamnatin kasar Zimbabwe ta tsai da cewa, za a shirya zabubukan hadin gwiwa na wannan karo daidai wa daida cikin adalci da kuma jituwa, shi ya sa har kullum ta yi kira ga bangarori daban daban masu shiga zabubukan da su kwantar da hankulansu. Sabo da haka gwamnatin kasar ta fitar da ka'idoji domin tabbatar da rashin samun al'amuran nuna karfin tuwo a gabanni da kuma bayan zabubukan.

Kwamitin zabe na kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, a ran 29 ga wata, masu zabe miliyan 5.6 da suka yi rajista za su jefa kuri'a a tashoshin jefa kuri'a fiye da 9000 a duk fadin kasar. Idan babu wani dan takarar neman zaman shugaban kasar da ya samu kuri'un da yawansu ya zarce kashi 50 cikin kashi dari, to za a shirya babban zabe na zagaye na biyu a cikin makwanni 3 masu zuwa.

Ra'ayin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, dalilin da ya sa zabubukan hadin gwiwa na kasar Zimbabwe suka jawo hankulan mutane sosai shi ne sabo da da farko, wannan shi ne karo na farko da kasar Zimbabwe ta shirya zabubukan shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki da kuma gwamnatocin wurare daban daban tare, kuma ba safai a kan ganin irin wannan hanyar zabe a kudancin Afirka ba. Domin ana iya shirya zabubukan hadin gwiwa kamar yadda ya kamata, a watan Satumba na shekarar da ta gabata, majalisar dokoki ta kasar Zimbabwe ta gyara tsarin mulkin kasar, da kuma zartas da wani kuduri bisa dukkan kuri'un nuna goyon baya a cikin wata daya da a wuce domin kaddamar da shirin gyara tsarin mulkin kasar.

Ban da wannan kuma, shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanar da cewa, zai ci gaba da neman zama shugaban kasar, wanda ya jawo hankalin gida da waje sosai. Shugaba Mubage da shekarunsa ya kai 84 da haihuwa yana daya daga cikin shugabannin Afirka da suka fi dadewa kan karagar mulkin kasa. A watan Disamba na shekarar da ta gabata, jam'iyyar ZANU-PF ta kasar Zimbabwe ta kira babban taron wakilan jam'iyyar, inda ta sanar da shugaba Mugabe da ya zama dan takarar shugaban kasar daya tak na babban zabe da za a yi a shekara ta 2008. Tun da Mugabe ya zama shugaban kasar a shekara ta 1987 har zuwa yanzu, ya riga ya kama mulkin kasar har kusan shekaru 28. Ko shakka babu, sanarwar da shugaba Mugabe ya yi wajen shiga babban zabe ta bata ran mutanen da suka nemi Mugabe da ya sauka daga kujerar mukin kasar sosai. Amma bisa halin da ake ciki yanzu, shugaba Mugabe dan takara ne mafi karfi.

Wani abin ban sha'awa daban na wannan babban zabe shi ne Simba Makoni, tsohon ministan kudi da na tattalin arziki wanda ya sanar da shiga babban zabe bisa matsayin dan takara mai zaman kai yau da wata guda da ya gabata, kuma ya samu goyon baya sosai. A matsayinsa na tsohon babban jami'in jam'iyyar ZANU-PF ta kasar Zimbabwe da kuma dan majalisar dokoki ta kasar, Mr. Makoni ya kalubalanci shugaba Mugabe a fili, wannan ya wuce tsammanin mutane da yawa. Wani ra'ayin bainal jama'a ya yi hasashen cewa, wannan ya shaida cewa, ana kasance da sabani cikin jam'iyyar ZANU-PF. Amma ana ganin cewa, Mr. Makoni ya samu goyon baya daga sauran rukunoni. Amma Mr. Makoni ya musunta dukkan hasashen da aka yi, kuma ya bayyana cewa, dalilin da ya sa ya shiga babban zabe shi ne sabo da yana fatan za a iya kara raya kasar Zimbabwe da kuma farfado da tattalin arzikinta.(Kande Gao)