Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 13:05:19    
Wani mugun wasa a gun biki mai kayatarwa

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, yau da kwanaki hudu da suka gabata, an gudanar da gagarumin bikin kunna wutar yola ta wasannin Olympics na Beijing a birnin Olympia na kasar Girka, inda wakilanmu suka ganam ma idanunsu yadda jama'a' kasar Girka suke nuna kyakkyawan fatan alheri ga gasar wasannin Olympics ta Beijing, inda suka kuma duba wani mugun wasa da ya barke a gun wannan biki mai kayatarwa.

In ba a manta ba, a wancan rana da safe misalin karfe 10, wato sauran awa daya kawai da ya rage a gudanar da bikin kunna wutar yola, dubban 'yan kallo sun zauna a kan dausayi mai ciyawa na filin wasan guje-guje na Olymmpics na can can zamanin da, wadanda zo daga wurare daban-daban na duniya, kuma yawancinsu Girkawa ne. Ministan al'adun kasar Girka Mr.Michalis Liapis ya furta cewa, a matsayin wani masomin wurin gudanar da wasannin Olympics, lallai jama'ar kasar Girka suka yi alfahari game da wannan; kuma bikin kunna wutar yola ya rigaya ya zama daya daga cikin bangarorin al'adun kasar. Jama'ar Girka na mayar da wannan rana a matsayin wata gagarumar ranar biki.

Da misalin karfe 11 na safiyar wannan rana, an soma gudanar da bikin kunna wutar yola. Ga rana na da haske; ga iska mai dadi. Bayan minti goma da wani abu na budewar bikin, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Sin Mr. Liu Qi ya yi jawabi, nan take wani mutum ya nufo Mr. Liu Qi da gudu tare da bude wani kyalle; akwai kuma sauran mutane biyu da suka shiga wannan mugun wasa. Amma 'yan sanda na Girka sun cafke su ba tare da bata lokaci ba. Mugun wasan da aka yi bai yi tasiri ga Mr. Liu Qi wajen yin gagarumin jawabi ba. A lokacin da Mr. Liu Qi ya kammala jawabinsa da kuma labarin cewa an yi nasarar kunna wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a gaban gidan ibada na Hera, nan take, ana ta yin tafi raf-raf don taya murna. An gudanar da bikin ne daidai bisa tsarin da aka kaddamar; kuma mugun wasan da aka yi ya samu suka daga jama'a masu kishin zaman lafiya da kuma wasannin Olympics na duniya.

Bayan lamarin, wakilanmu sun samu labarin cewa ,wadancan mutane uku sun zo ne daga wata kungiyar da ake kira " Reporters Wathout Borders". Dalilin da ya sa suka gudu daga binciken tsaro na bangaren 'yan sandan Girka, shi ne saboda su 'yan jarida ne da suka yi rajistar daukar labarai. Lallai sun aikata danyen aiki da bai ya dace da asalin sana'arsu ba; kuma zamba ce suka yi.

Mutane na ganin cewa, sun yi wannan mugun wasa ne domin bayyana ra'ayinsu na siyasa da zummar saka harkokin siyasa cikin gasar wasannin Olympics, da kuma shafa bakin fenti ga wasannin Olympics na Beijing. Saboda haka ne dai, mutane daga bangarori daban-daban suka yi Allah wadai da irin danyen aikin da suka yi. Mataimakin shugaba kuma dan asalin kasar Girka na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa Mr.Lambis Nikolaou ya fadi cewa: " Lallai na kadu da fusata saboda wadannan mutane ba su mutumta inda suke ba". Ban da wannan kuma, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa Mr. Jacques Rogger ya sha jaddada cewa gasar wasannin Olympics ba hukumar siyasa ba ce. Bayan aukuwar lamarin, ya furta cewa: " Na yi bakin ciki matuka da ganin an haifar da tsaiko ga bikin da ake gudanarwa". Bugu da kari, shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Girka Mr.Minos Kyriakou ya nuna bacin rai sosai cewa ya yi lallai ana saka harkokin siyasa da dama cikin fannoni daban-daban; ko ta yaya kada a sake sanya wannan gasar wasannin Olympics da jama'ar duk duniya ke sha'awarta kwarai da gaske cikin tarkon siyasa! Wani jami'in sashen watsa labarai na Girka ya fada wa wakilanmu cewa, danyen aikin da wadannan mutane suka aikata ya lahanta halin tsarki na bikin kunna wutar yola. Dadin dadawa, mataimakin shugaban kwamitin kula da daidaita harkokin wasannin Olympics na shekarar 2008 na kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa Mr.Richard Gosper ya fadi cewa: " Gasar wasannin Olympics na alamata fitattun wasannin motsa jiki, da zaman lafiya da kuma zumunci. Ko da yake akwai wassu mutane dake nufin shuka barna da yin zargi da gangan, amma duk da haka muna fatan za a cimma nasara wajen mika wutar yola ta wasannin Olympics a matsayin akida da kuma hasashen wasannin Olympics". (Sani Wang )