Gwamnatin kasar Sin za ta samar da jari mai yawa domin kiyaye muhallin jihar Tibet.
Bisa labarin da aka samu daga hukumar kiyaye muhalli ta jihar Tibet, an ce, wannan "shirin kiyaye muhalli na tudun Tibet" zai kashe RMB yuan fiye da biliyan 10, ya hada da ayyuka guda 14 tun daga shekarar 2006 zuwa shekarar 2030, ciki har da yaye filin ciyayi na halitu, da kiyaye muhallin abubuwan halitta masu rai ko marasa rai, da ayyukan tinkarar zaizayaewar ruwa da sa.
An ce, za a maido da filin ciyayi kusan kadada miliyan 15, da kuma kyautata zaizayewar kasa iye da kadada miliyan 3.1 a cikin wannan shiri.
|