'Yan jarida wadanda suka ga al'amarin Tibet da idonsu sun nuna rashin jin dadi da kuma yin kakkausar suka ga wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammaci da suka murde gaskiya.
Wani da aka yi abin kan idanunsa mai suna Kelzang Dawa 'dan jarida na kamfanin dillancin watsa labaru na Xinhua ya ce, ya ga masu tada hankula sun yi laifuffuka yadda suka ga dama. Amma wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammaci sun murde gaskiya na al'amarin Tibet, wannan ya nuna munafancinsu a fili na wai "bayar da labaru bisa gaskiya". Kelzang Dawa ya nuna cewa, shi ani 'dan jarida ne kuma wani matashi dan kabilar Tibet ne, ba ya son garinsa ya zama wani wurin ta'addanci, kuma ba ya son mutanen garinsa su damu da zaman rayuwa.
A ran 14 ga wata da yamma, Mr. Zhang Shaohong wakilin gidan telebijin na kasar Sin, wato CCTV, ya tafi titin Bakuo da ke birnin Lhasa, ya ga yadda aka lalata halin bunkasuwa da ake ciki. Ya ce, yayin da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammaci suke bayar rahotanni kan al'amarin Tibet, ba su lura da gaskiya ba, sunn ba da rahotanni marasa gaskiya, wannan ya karya da'a ta aikin watsa labaru.
|