Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-28 10:21:11    
An kammala ayyukan rana ta hudu wajen mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a kasar Girka lami lafiya

cri

An kammala ayyukan rana ta hudu wajen mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 a kasar Girka yadda ya kamata jiya 27 ga wata.

Da karfe 9 da rabi na safe, agogon wurin ne, aka fara mika wutar yola ta gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing daga birnin Veria dake arewacin Girka zuwa arewa maso gabashin kasar. Bayan da aka ratsa birane 7, ciki har da Naoussa, da Skidra, da Edessa, da misalin karfe 7 da minti 24 na dare ne aka kai wutar yola birnin Thessaloniki, tashar jiragen ruwa mafi girma a arewacin Girka, kuma babban birni na biyu a kasar, inda aka shirya gagarumin bikin maraba da zuwan wutar yolar.

Za a kai wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekarar 2008 babban birnin Girka wato Athens a ranar 30 ga watan da muke ciki, inda za a shirya bikin mika wutar, domin mika wutar yola ga birnin Beijing mai masaukin gasar wasannin Olympics a hukumance.(Murtala)