Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 20:36:13    
A tsanake ne, kasar Sin tana tsayawa kan adawa da ko wace kasa da ta tsoma baki cikin harkokin gida na Sin

cri

A gun taron manema labaru da aka shirya a ran 27 ga wata a birnin Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mr Qin Gang ya bayyana cewa, a tsanake ne, kasar Sin tana tsayawa kan adawa da ko wace kasa da ta tsoma baki cikin harkokin gida na Sin, gwamnatin kasar Sin tana da niyya, kuma tana da kwarewar kare mulkin kai da cikakken yankin kasa.

Wani manemin labaru ya ce, a 'yan kwanakin baya, an ce, hukumar leken asiri ta kasar Amurka wato CIA ta jagoranci kuma ta shiga cikin tashe tashen hankula a birnin Lhasa, mai yiyuwa ne wata babbar kungiyar duniya tana ba da taimakon kudi game da haka. Mene ne ra'ayin kasar Sin ?

Mr Qin ya ce, tun fil azal, jihar Tibet ta zama wani kashi na kasar Sin, harkokin Tibet harkokin gidan Sin ne, a tsanake ne, gwamnatin kasar Sin take tsayawa kan adawa da ko wace kasa da ta tsoma baki cikin harkokin Tibet da sauran harkokin gida na Sin.

Mr Qin ya jaddada cewa, kasar Sin ta bukaci kasashen da abin ya shafa da su girmamawa mulkin kai da cikakken yankin kasar Sin, kuma su bi ka'idar da ke tsakanin kasa da kasa, kada su nuna goyon baya ta ko wace hanya bisa ko wace fakewa ga ayyunkan neman baraka da rukunin Dalailama yake yi. Gwamnatin kasar Sin tana da niyya, kuma tana da kwarewar kare mulkin kai da cikakken yankin kasa.(Danladi)