Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 16:24:19    
Lamarin ran 4 ga watan Maris da ya auku a birnin Lhasa na Sin ya tone makarkashiyar rukunin Dalai Lama ta lalata addini

cri
A kwanakin nan, bi da bi manyan malamai da dawamamun 'yan addinin Buddha na jihar Tibet ta kasar Sin sun bayyana cewa, al'amarin tashe-tashen hankali mai tsanani na kai farmaki kan jama'a da farfasa kayayyaki da wawashe su da kuma sanya wa wurare wuta ya auku a birnin Lhasa a ran 14 ga wata, sosai da sosai ya tone makarkashiyar da rukunin Dalai Lama ya kulla don lalata addini.

Dawamammen dan addinin Buddha Lhadar Ngagwang Daindzin, mataimakin shugaban reshen Tibet na kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin ya ce, Dalai Lama ya yi amfani da matsayinsa kan addini wajen tunzura wasu 'yan addinin Buddha da suka tada tarzoma iri daban daban a yankunan kasar Sin. Ba ma kawai tarzomar ta lalata tsarin addinin da ake bi yadda ya kamata ba, har ma ta saba wa darikar addinin Buddha.

Dawamammen dan addinin Buddha Dupkang Tupden Kedup, shugaban reshen Tibet na kungiyar addinin Buddha ta kasar Sin shi ma ya ce, bisa matsayinsa na addinin Buddha, ya yi matukar bakin ciki da ganin yadda mutane masu sanye da jan kayan addinin Buddha suka kai hari kan jama'a da farfasa kayayyaki da wawashe su da kuma sa wurare wuta ba ji ba gani. Ya yi kira ga dawamammun 'yan addinin Buddha da manyan malaman addini na gidajen Ibada manya da kanana na jihar Tibet da su gane makarkashiyar da 'yan a-ware suka kulla, su kuila da gidajen ibadansu da kyau, kuma su yi wa mabiyansu tarbiyya sosai.

Lobsangba Chilai Qoisang, dawamammen dan addinin Buddha na gidan Ibada mai suna Qamdo ya bayyana cewa, a cikin shekaru sama da goma da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta zuba makudan kudade wajen yin kwaskwarima a kan gidajen Ibada, ta ba da taimakon kudi ga tsoffin 'yan addinin Buddha, amma 'yan addinin kalilan ba su saka mata alheri ba, kuma sun saba wa darikar addini, wannan ya bakanta ran mutane kwarai. (Halilu)