Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 16:18:36    
Kasar Sin ta juya hankali musamman kan shiyyoyin noma da kiwon dabbobi wajen ba da gudummawa ga jihar Tibet

cri
Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta juya hankalinta daga birane da garuruwa zuwa shiyyoyin noma da kiwon dabbobi wajen matakan da ta dauka da kuma kudin da ta ware domin ba da gudummawa ga jihar Tibet, ta yadda zaman rayuwar manoma da makiyaya na jihar Tibet ya samun kyautatuwa sosai.

Yawan manoma da makiyaya ya wuce kashi 80 cikin 100 bisa dukkan mutanen jihar. Tun shekarar 2006 zuwa yanzu, jimlar kudin da jihar Tibet ta ware domin tsugunar da manoma da makiyaya ta wuce kudin Sin wato Yuan biliyan 1.7, daga cikin kudaden fiye da Yuan biliyan 3 da za a ware cikin shekaru 3 masu zuwa domin ba da gudummawa ga jihar kuma, yawancinsu za a yi amfani da su ne domin sa kaimi ga aikin tsugunar da mayawata masu kiwo, da daukar mutane masu yaki da kangin talauci zuwa sabbin gidaje, da kuma kyautata lalatattun gidajen manoma, ta yadda zuwa shekarar 2010, za a yi kokarin daukar manoma da makiyayya fiye da kashi 80 bisa 100 na jihar Tibet cikin gidaje masu inganci, kuma za a rubanya kokari domin yin muhimman gine-gine, da kara saurin bunkasa harkokin ba da ilmi da kiwon lafiya da al'adu. (Umaru)