Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:18:56    
Bil adam na mayar da abinci a matsayin sama

cri

Tun fil azal akwai wata karin magana a nan kasar Sin, wato "Bil adam na mayar da abinci a matsayin sama", ma'anar "sama" a nan ita ce, abin da ya fi muhimmanci, wato ana iya cewa, "cin abinci" bukata ce ta farko ta bil Adam a cikin zaman rayuwarsu. A cikin shirinmu na yau, bari mu kusanci wasu 'yan majalisar wakilai musulmi da suka halarci taro a zaman farko na majalisar wakilai ta jama'ar kasar Sin a karo na 11 da aka shirya a kwanan baya a nan birnin Beijing, kuma bari mu fahimci sauye-sauyen musulmi a fannin cin abinci tun shekaru 30 da suka wuce, wato tun bayan da aka yi gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin.

A lokacin da yake waiwayen halin da ake ciki yau da shekaru 30 da suka wuce, Ashar Tursun, 'dan majalisar wakilai daga kabilar Uygur da ke da shekaru 45 na haihuwa ya ce, a lokacin da kyar ake iya samun abinci masu dadin ci.

"Yau da shekaru 30 da suka wuce, mu kan yi farin ciki idan mun samu isashen abinci."

Ga mutane na karni 60 zuwa karni 70, kunun da aka yi da masara, da burodin tururi, da kuma kayan lambu da aka dafa tare da mai kadan, dukkansu ba kawai su ne abinci kawai ba, har ma sun zama wata alama ta zamanin. Bisa al'adar cin abinci ta lokacin, ko kana so ko ba ka so, babu sauran zabi ba, sai dai ka karbi wannan hakikanin hali, wato cin irin wannan abinci.

Shehun malami Abdulah. Abbas, 'dan majalisar wakilai daga kabilar Tatar, ya ce, "A da, ba mu iya cin nama ba sai dai a lokacin babbar salla, saboda haka, muna sa ido ga zuwan babbar salla."

Babbar salla, wani gagarumin biki ne ga kananan kabilu masu bin addinin musulunci na kasar Sin, kamar su kabilun Hui, da Uygur, da Hazak, da Ozbek, da Tajik, da Tatar, da Kirgiz, da Sala, da Dongxiang, da kuma Bao'an, da dai sauransu. Bisa shari'ar musulunci, a lokacin babbar salla, a kalla dai ko wane iyalin musulmi kan yanka tunkiya daya, wasu lokuta kuma su kan yanka shanu, ko rakumi, da kuma dawaki, da dai sauransu. Amma, saboda halin tattalin arziki da ake ciki a lokacin, ba mai iyuwa ba ne a yanka tunkiya daya yau da shekaru 30 da suka wuce. 'Dan majalisar wakilai Su Guanglin, wato mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta birnin Lanzhou na lardin Gansu, kuma mataimakin shugaban majalisar musulunci ta birnin Lanzhou, ya waiwayo cewa, "Ana bukatar yanka tunkiya a lokacin babbar salla, a da idan an kashe kudi kadan za a iya sayen tunkiya daya, lallai akwai araha sosai, amma musulmin da suka yanka tunkiya a da ba su da yawa, saboda mun yi fama da talauci a lokacin."

A karni na 70, ba a iya samun isasshen kayayyakin zaman rayuwa ba, saboda haka, a lokacin da mutane ke sayen kayayyaki, ban da biyan kudi, kuma tilas ne su nuna tikitoci na iri daban daban. Kamar tikitin mai, da na hatsi, da dai sauransu. Wang Xiaoke, 'yar majalisar wakilai daga kabilar Hui ta gaya mana cewa, "A lokacin, iyaye na su ne malamai, kuma babu yara da yawa a iyalinmu, saboda haka, zaman rayuwarmu ya yi kamar yadda ya kamata. Amma, saboda kasarmu ba ta iya samar da arzikin kayayyaki ba, don haka, ko da ya ke kana da kudi, amma ba ka iya sayen kayayyakin da kake so ba."

Manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga gasashen waje da kasar Sinke dauka, ta sanya jama'ar kasar Sin su shiga zaman al'umma mai wadata daga halin rashin samun isasshen abinci da sutura. Kan wannan sauyawa, 'yar majalisar wakilai daga kabilar Ozbek Halitan Nur Maimaiti ta ce, "A da, babu kayan lambu na iri da yawa ba, amma ya zuwa karni na 80, halin nan ya canjawa."

A karni na 90, bisa kara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, da kuma bunkasuwar tattalin arziki a nan kasar Sin, an biya bukatun Sinawa a fannin cin abinci. Ciki kuwa, ba kawai abincin musulmi na kasar Sin suna biyan bukatun musulmi na kasar Sin ba, har ma sun fita waje, sun bullo a teburin cin abinci na musulmi na kasashen Larabawa. A waje daya kuma, abinci na kasashen Faransa da Japan, da kuma sauran kasasshe, su ma sun shiga kasuwar kasar Sin daya bayan daya. Saboda haka, Sinawa suna iya cin abinci masu dadinci na kasashen duniya, amma ba tare da fita waje ba. Amma, arzikin abinci ya sanya Sinawa da su sake yin tunani kan abinci. Jin Lanying, 'yar majalisar wakilai daga kabilar Hui ta ce, "Yanzu, mu kan ci abinci kamar nama, da kifi, da dai sauransu, a sakamakon haka, da sauki muke iya samun ciwace-ciwace, ciki har da kitse da ke cikin jini ya yi yawa fiye da kima"

Yanzu, mutane suna kara mayar da hankali kan lafiyar jiki a fannin cin abinci, a lokacin da suke sayen abinci a kasuwa, kullum suna kulawa da ingancin abinci. A sanadiyar haka, abincin da suka fi gina jiki suna ta kara samun karbuwa.