Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:12:38    
Nune-nunen da aka shirya kan sakamakon da nakasassu suka samu

cri

A 'yan kwanakin baya a birnin Nanjing na lardin Jiangsu, an yi nune-nunen sakamakon da nakasassu na duk kasar Sin da na shiyyar gabashin kasar Sin suka samu , wadannan shahararrun sakamakon da nakasassu suka samu da bayyanuwar fasahar da nakasassu kwararru a sana'o'in musamman suka yi wa duk zamantakewar al'umma sun bayyana cewa, nakasassu su ne masu kago dukiyoyin kayayyaki da na tunani na duk dan adam tamkar yadda kowa yake yi .A karkashin hasken rana gu daya, suna da buri daya da na sauran mutane masu koshin lafiya don neman abubuwa masu kyau wajen zaman rayuwa da fasahohi da sauransu .

A gun nune-nunen nan da aka shirya, an nuna ingantattun kayayyakin fasaha fiye da 500 da nakasassu suka yi kuma larduna da birane da jihohi masu aiwatar da harkokin kansu 19 na duk kasar Sin suka aika ciki har da duwatsu da katako da aka sassaka da littatafan kan sarki da sauran kayayyakin fasaha, ciki har da wasu sun sami manyan lambobin yabo na kasashen duniya da na kasar Sin. A sa'I daya kuma, nakasassu fiye da 20 da suka zo daga shiyyar gabashin kasar Sin sun nuna fasahohinsu na yin abubuwa a wurin nune-nunen, alal misali, makafi sun nuna fasahohinsu na harhada injuna masu kwakwalwa da na yin kayayyakin fasaha da hannayensu na kansu da kuma wadanda hannayensu suka nakasa sun nuna fasaharsu na kera tukwane da sassaka abubuwa da yanke takardu da kafafuwarsu , kai fasahohinsu masu kyau sosai sun bayyana kishin zaman rayuwa da nakasassu suka yi da kuma bege mai kyau da suka yi ga makomarsu ta nan gaba. Nune-nunen nan ya jawo hankulan rukunoni da 'yan kallo masu yawan gaske, a wurin yin nune-nunen, ana ta ihu da yin tafi raf raf.

Dazun nan kidan da kuka ji kida ne da aka yi da piyano, wani makaho ne ya kada, sunansa Liu Qi, yanzu, yana da shekaru 22 da haihuwa, shi wani dalibi ne na wani kolejin makafi na birnin Nanjing. Tun daga lokacin yarantakarsa, yana kishin wake wake da kade-kade, lokacin da ya kai shekaru 12 da haihuwa, ya fara koyon ilmin kada piyano, amma lokacin da ya kai shekaru 14 da haihuwa, ya makance bisa sanadiyar raunin da aka yi masa, amma bai bar koyon ba, bayan jurewar wahaloli masu yawan gaske da ya yi wajen horon da aka yi masa, sai matsayinsa na yin wasan piyano ya kai mataki na goma, kuma daga shekarar 2001 zuwa 2003, ya yi wasan kada piyano tare da shahararen dan wasan piyano mr Lichard Klaideman na kasar Faransa a gun wurin wasa daya har sau uku, inda ya sami matukar maraba da yabo sosai daga wajen 'yan kallo.Yanzu, mr Liu Qi ya yi gwajin rubuta kade-kade. Da muka ganin wasan da ya yi na kada piyano, sai muka ji kamar duniya mai kyau a cikin zuciyarsa.

Malam Yin Jian Nan wanda hannunsa ya nakasa ya ji dadi sosai a gun wurin nune-nunen, yana hira yana dariya tare da sauran mutane, ya sami sakamako mai kyau wajen yin zane-zane da sassaka abubuwa, fasahohin da ya yi sun fi na sauran mutane masu koshin lafiya. Yanzu ya zama mamban hadadiyyar kungiyar kwararrun zane-zane ta kasar Sin da mamban majalisar kamfanin madaba'ar Nanjing, ya taba shiga nune-nunen kasashen duniya a jeri, kuma ya sami lambobin yabo da yawa. A gaban babban sakamako da ya samu, ya ji kunya da cewa, sakamakon da na samu a yanzu ba ya rabuwa da goyon baya da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da rassanta dabam daban suka yi ba, a kodayaushe na ke tsammani cewa, bisa matsayin nakasassu, dayake na samu sakamako ko babba ko karami,dole ne na mayar wa zamantakewar al'umma da jama'a . Yanzu, ina cikin halin samartaka, ya kamata in kara kago makoma mai kyau na nan gaba cikin himma da kwazo ba tare da kasala ba . wadannan lambobin yabo da aka ba ni sun shaida abubuwan da na yi a da kawai, amma ba su bayyana abubuwan da zan yi a nan gaba ba.Yin nazari kan ilmi da fasaha ba ya da iyaka, ya kamata a yi koyo har abada.

A wurin nune-nune, an kuma ga dalibai masu aikin bautawa da suka sanya shirt masu launin rawaya da yawa, wata daliba mai suna Sun Yu Jiao ta jami'ar koyon ilmin magungunan sha na gargajiyar kasar Sin ta burge sosai bisa halin da nakasassu suka yi na fid da tsoro da nuna bajinta ba tare da kasala ba, ta gaya wa manema labaru cewa, a wannan gami, muhimman ayyukan da suka yi su ne samar wa nakasassu da suka shiga nune-nunen taimako a fannoni dabam daban, amma wadannan nakasassu su kan kin taimakon da muka yi musu, wato su kan yi abubuwa su da kansu.