A ran 26 ga wata da safe, an sake bude kofar fadar Potala da ke birnin Lhasa na jihar Tibet inda hasken rana ya yi kal. Bayan mummunan tashin hankalin da aka haddasa a ran 14 ga wata, an rufe kofar ala tilas.
An ce, yawan masu ziyarar da aka karba a ran 26 ga wata a fadar ya kai kusan 100, daga cikin su da akwai masu yawon shakatawa 24, sauransu kuwa mutane masu bin addinin Budda na wannan wuri ne.
Fadar Potala tana kan wani tudun da ke da nisan kimanin mita 2000 daga arewa maso yammacin birnin Lhasa, yau fadar nan ta yi shekaru 1300 da ginawa, ita shahararren gini ne na tsohon zamanin kasar Sin, kuma muhimmin sashen kayayyakin tarihi ne da ya samun kariya daga duk kasar Sin. (Umaru)
|