Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:05:56    
Al'amuran aikata laifuffuka da aka tayar a jihar Tibet sun keta hakkin bil Adama na fararen hula na kabilu daban daban na jihar

cri
A ran 26 ga wata, wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin ya bayar da sharhi, inda ya nuna cewa, al'amuran aikata laifuffuka da aka tayar a jihar Tibet mai cin gashin kai ta kasar Sin sun keta hakkin bil Adama na fararen hula na kabilu daban daban na jihar sosai.

Sharhin ya bayyana cewa, al'amuran aikata laifuffuka sun yi sanadiyar mutuwar fararen hula 18 yayin da mutane 382 suka jikata, dakunan kwana na fararen hula 120 sun kone. Haka kuma an kwace da kuma kuna kantuna 908 da makarantu 7 da kuma asibitoci 5. Dukkan wadannan abubuwa sun bayyana makircin da rukunin Dalai Lama ya kulla. Haka kuma wadannan al'amuran aikata laifuffuka da aka tayar a ran 14 ga wata a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet sun gaya mana cewa, al'amuran sun keta hakkin bil Adama na fararen hula na kabilu daban daban na jihar sosai.

Bugu da kari kuma sharhin ya nuna cewa, a hakika dai, ainihin burin rukunin Dalai Lama da ya daga tutar wai kiyaye hakkin bil Adama shi ne neman 'yancin kan Tibet da kuma maido da tsarin bauta na gargajiya da ke hada mulkin kai da addini tare a jihar. Idan makarkashiyar rukunin Dalai Lama ta ci nasara, to jama'ar Tibet za su gamu da wani bala'in hakkin bil Adama. Amma kungiyoyi kalilan da suka kulla makarkashiya ba za su hana ci gaban tarihi ba.(Kande Gao)