Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 15:04:13    
Rana ta uku ta mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing a kasar Girka

cri

A ran 26 ga wata, an kammala aiki na rana ta uku na mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing ta shekara ta 2008 a kasar Girka.

A ran nan da karfe 9 da safe bisa agogon wurin, an fara mika wutar yola ta gasar wasannin Olympcis ta Beijing daga birnin Janina da ke tsakiya kasar Girka zuwa arewa maso gabas. Kuma bayan da ta ratsa biranen Metsovo da Grevena da Kozani, a karshe dai wutar yola ta isa birnin Veria a ranar da karfe 5 da minti 35 da yamma, inda ta yada zango a wurin. A cikin wadannan birane, birnin Metsovo yana kan tudu, kuma tsayinsa ya kai mita 1200 daga leburin teku. Wutar yola ta wasannin Olympics ta Beijing ta ratsa duwatsun da kankara mai laushi ta rufe su tare da nasara, ta isa wurin bayan da aka jure wahalolin kankara da kuma yanayin sanyi.

Lokacin da ake yin aikin mika wutar yola, mazaunan biranen sun yi marhabin zuwan wutar yola da hannu biyu biyu. Sun fito daga gidaje da kuma shirya bukukuwan da ke da halin musamman na wurin don nuna maraba da zuwan wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing. A ran 27 ga wata, wutar yola za ta ratsa birane 7 na kasar Girka, shi ya sa za a sha aiki sosai.(Kande Gao)