Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 14:38:21    
Gasar wasannin Olympic na Beijing za ta ci gaba da yadada ra'ayin wasannin Olympic

cri
Ran 26 ga wata rana ce ta uku da aka fara mika wutar gasar wasannin Olympic a kasar Greece. Shugaban birnin Grevena na kasar Greece dake kan hanyar mika wutar Mr. Giorge Nutsos ya bayyana a gun wurin da aka mika wutar cewa, gasar wasannin Olympic na Beijing za ta ci gaba da yadada ra'ayin wasannin Olympic.

An fara mika wutar ta gasar wasannin Olympic na Beijing a birnin Janina a ran nan da karfe 9 da safe bisa agogon wuri, kuma an kai ta birnin Grevena da karfe 1 da minti 45 da yamma. Wannan ya zama karo na biyu da wutar ta kai wannan karamin birni dake da mutane dubu 20 kawai tun da shekarar 2004.

Mr. Nutsos ya ce, al'adun Sin da Greece masu dogon tarihi sun hadu a nan ta hanayr mika wutar wasannin Olympic na Beijing. Wutar yola ta wasannin Olympic ta bayar da ra'ayin zaman tare cikin lumana ga mutanen duniya. Zaman lafiya ba batu ne na 'yan kwanaki masu zuwa, sai ya kamata a dauke shi a matsayin batu na din din din. (Zubairu)