Jiya 26 ga wata da dare, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi hira da takwaran aikinsa na kasar Amerika George W. Bush ta wayar tarho.
Dangane da batun Taiwan, shugaba Hu ya nuna yabo ga shugaba Bush da gwamnatinsa kan matsayin da suke tsayawa a kai, wato sau da dama ne suka bayyana cewar suna tsayawa tsayin daka kan manufar "kasar Sin daya tak a duniya", da bin hadaddiyar sanarwa guda uku da aka daddale tsakanin Sin da Amerika, da nuna adawa ga yunkurin raba Taiwan daga kasar Sin, da na jefa kuri'ar raba gardama kan shigar Taiwan cikin Majalisar Dinkin Duniya, da nuna adawa ga hukumar Taiwan kan yunkurinta na neman shiga cikin wasu kungiyoyin kasa da kasa wadanda kasashe masu mulkin kai ne kawai ke iya shiga. Shugaba Hu Jintao yana fatan bangarorin biyu wato Sin da Amerika za su cigaba da yin kokari wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.
A waje daya, game da munanan laifuffukan da aka aikata a babban birnin Tibet wato Lhasa kwanan baya, wato yin duke-duke, da fasa kayayyaki, da kwace kayayyaki, tare da cunnawa kayayyaki wuta, shugaba Hu Jiantao ya yi nuni da cewar, duk wata gwamnati mai daukar alhaki ba za ta kyale masu tarzoma su keta hakkin dan Adam, da yin zagon-kasa ga doka da oda ta zamantakewar al'umma, da kawo babbar illa ga zaman rayuwar jama'a da dukiyoyinsu ba.
Shugaba Hu ya jaddada cewar, gwamnatin kasar Sin tana fatan cigaba da yin tuntuba da shawarwari tare da Dalai Lama, muddin ya yi watsi da duk wani yunkurinsa na neman 'yancin kan Tibet, da daina aika-aikar kawowa kasar Sin baraka ba tare da bata lokaci ba, musamman ma danyen aikinsa na tada tashe-tashen hankula da gangan a Tibet da yin zagon-kasa ga gasar wasannin Olympics ta Beijing, tare kuma da amince da cewa Tibet da Taiwan dukkansu bangarori ne da ba za a iya raba su daga kasar Sin ba.(Murtala)
|