Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-27 11:01:22    
Kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympics ta Nijeriya ta sami takardar izni ta karshe wajen halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing

cri
A gun gasar wasan kwallon kafa ta fidda gwani a gasar wasannin Olympics ta Beijing ta 2008 ta shiyyar Afirka wadda aka yi a jiya 26 ga wata, kungiyar wasan kwallon kafa ta Nijeriya mai masaukin wasan ta lashe ta Afirka ta Kudu da ci uku da banza, wadda ta kasance kungiyar wasan kwallon kafa ta karshe wajen samun takardar iznin halartar gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta Beijing.

Bayan gasar, kungiyar Nijeriya na kan gaba a rukuninta, wadda ta ba kungiyar Ghana ratar maki 1. Saboda haka ne, kungiyar wasan kwallon kafa ta Nijeriya ta cimma nasarar samun takardar iznin halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing, wadda ta kasance kungiya ta karshe wajen samun iznin halartar gasannin karshe na wasan kwallon kafa na gasar wasannin Olympics ta Beijing. Tuni, kungiyar wasan kwallon kafa ta Kamaru da ta Kwadivwa sun riga sun sami izinin halartar gasar wasannin Olympics ta Beijing.(Murtala)