A ran 26 ga wata da safe, tawagar manema labaru na gida da waje da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya ta tashi daga birnin Beijing zuwa birnin Lhasa, babban birnin jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokinsa da kanta, domin neman labaru dangane da tashe tashen hankali da suka faru a ranar 14 ga wata.
Wannan tawaga ta hada da manema labaru da suka zo daga kafofin watsa labaru guda 19, wato kamfanin dillancin labaru na Associated Press ta kasar Amurka, da jaridar Financial Times ta kasar Ingila, da kamfanin dillancin labaru na TACC na kasar Rasha, da kamfanin watsa labaru na Kyodo News na kasar Japan, da gidan TV ta KBS na kasar Korea ta kudu, da gidan TV na Qatar, da jaridar China Daily ta kasar Sin, da kuma jaridar Beijing weekly da dai sauransu.
Tawagar manema labaru za ta shafe kwanaki 3 tana neman labaru a birin Lhasa.(Danladi)
|