Yau Laraba, Mr Qin Gang, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, gwamnatin kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen yin adawa da dukkan harkokin da Dalai ke yi bisa matsayinsa a sauran kasashe don nema jawo wa kasar Sin baraka, kuma tana tsayawa tsayin daka wajen yin adawa da ma'amalar da gwamnatocin dukkan kasashe ke yi tare da Dalai ta ko wace hanya.
Wani manemi labaru ya tambaya cewa, bisa labarin da aka bayar, Bernard Kouchner, ministan harkokin waje na kasar Faransa ya ce, ba ya iya hakuri da dannewar da kasar Sin ta yi a Tibet. Yarde, sakatariyar ma'aikatar harkokin waje na kasar Faransa mai kula da harkokin waje da na hakkin dan adam ta furta cewa, idan Dalai ya kai ziyara a kasarsa, to, ko shakka babu za ta gana da shi. Ina ra'ayin bangaren Sin a kan wannan?
Mr Qin Gang ya amsa cewa, al'amarin Lhasa ta'asar da rukunin Dalai ya shirya kuma ya tayar da gangan don neman jawo wa kasar Sin baraka. Gwamnatin kasar Sin ta dauki mataki bisa doka don mayar da al'amaru a birnin Lhasa da sauran waurare kamar yadda ya kamata. Ya kamata, dukkan kasashen da ke nuna adalci da gaskiya su nuna fahimta da goyon baya ga kasar Sin, bisa wajabtaccen matakin da ta dauka yadda ya kamata don kiyaye zaman karko da rayuwar jama'a da dukiyoyinsu. Qin Gang ya kara da cewa, tarzomar da ta auku a birnin Lhasa ta sake nuna cewa, ko kusa, Dalai ba wani dan addani ne da a kan gani ba, shi wani dan gudun hijirar siyasa ne, a karkashin fakewa da addini da zaman lafiya, ya dade yana neman jawo wa kasar Sin baraka, da lalata hadin kan kabilu da zaman lafiyar jama'a. (Halilu)
|