Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 20:19:59    
Bisa goyon bayan jama'ar kasashe daban daban, tabbas ne za a cimma nasarar gudanar da wasannin Olympics na Beijing, in ji kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin

cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Qin Gang ya bayyana a yau 26 ga wata a nan birnin Beijing cewa, bisa goyon bayan jama'ar kasashe daban daban, tabbas ne za a cimma nasarar gudanar da wasannin Olympics a birnin Beijing.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a yayin da shugaba Sarkozy na kasar Faransa ke amsa tambayoyin manema labarai game da ko zai kaurace wa wasannin Olympics na Beijing, ya ce, yanzu ba za a iya kebantar da duk wani zabi ba.

A yayin da Mr.Qin Gang ke amsa tambayoyin manema labarai a game da furucin, ya ce, wasannin Olympics na Beijing na shekarar 2008 ba ma kawai wani kasaitaccen biki ne ga dukan jama'ar kasar Sin, haka kuma gaggarumin biki ne na jama'ar duniya baki daya. Muna fatan wasannin zai iya karfafa fahimtar juna da zumunci da hadin gwiwa a tsakanin jama'ar kasashe daban daban. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata mu bi manufar wasannin Olympics, kada a mayar da shi a siyasance.(Lubabatu)