Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 18:19:39    
Kasar Sin tana binciken lamuran karya doka na neman samun kuri'a ta hanyar ba da cin hanci

cri

A ran 25 ga wata a birnin Beijing, kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da Ma'aikata mai kula da harkokin shirin kungiyoyi na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun shirya wani taro cikin hadin gwiwa, inda aka sanar da bayani kan binciken lamuran karya doka yayin da wurare daban daban na kasar Sin suke canza shugabanninsu. Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin shekara daya da ta wuce, hukumomi na matakai daban daban na kasar Sin masu kula da harkokin da'a sun yanke hukunci kan laifuffuka 1900 a lokacin da aka canza shugabannin kwamitocin jam'iyyar, da majalisun wakilan jama'a, da gwamnatoci, da majalisun ba da shawara kan harkokin siyasa na wurare daban daban, an yanke hukunci kan jami'ai da yawansu ya kai 1948. Jami'an kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da Ma'aikata mai kula da harkokin shirin hukumomi na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun bayyana cewa, binciken lamuran karya doka da yanke hukunci kan wadanda suka karya doka sun tabbatar da gudanar da aikin canza gwamnatoci cikin ruwan sanyi.

Zaunannen mamban kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, kuma mataimakin minista mai kula da harkokin shirin hukumomi na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wato Mr Zhang Jinan ya gaya mana cewa, a lokacin da ake canza gwamnatoci, kasar Sin ta inganta sa ido da bincike kan aikin zabuka. Ya ce,

'A lokacin da majalisu biyu na larduna da jihohi daban daban na kasar Sin suke zamansu, kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da Ma'aikata mai kula da harkokin shirin hukumomi na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun tura kungiyoyin sa ido da yawansu ya kai 20 zuwa larduna da jihohi 31, domin jagorantar wurare daban daban da su aiwatar da manufofi da dokoki da abin ya shafa, ta yadda za a tafiyar da ayyukan zabuka yadda ya kamata. Wannan ya zama karo na farko da aka tura kungiyoyin sa ido kan ayyukan zabuka a yayin da ake shirya tarurrukan majalisun biyu.'

Mataimakin sakataren kwamitin tsakiya mai kula da harkokin da'a na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin wato Mr Huang Shuxian ya bayyana a gun taron cewa, a nan gaba, kasar Sin za ta kara inganta da'ar shugabanni na wurare daban daban, domin su tafiyar da mulkinsu ba tare da cin hanci da rashawa ba. A sa'i daya kuma, kasar Sin za ta kyautata tsarin zabukan jami'ai da kuma nada su. Ya ce,

'A halin yanzu, da kuma a wani wa'adi mai zuwa, kasar Sin za ta kara kyautata tsarin gabatar da sunayen jami'ai da kuma nada su, da kuma kyautata tsarin da ke dangane da wa'adin jami'ai da kuma yin mu'amala da su, da kuma kyautata tsarin kimantawar jami'ai domin ya biya bukatar ra'ayin samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya, da kuma kyautata ayyukan zabuka a fili, da kuma yin takara, da gudanar da tsarin 'yan takara sun fi guraben masu cin takara yawa.'(Danladi)