Jiya 25 ga wata, magajin garin birnin Ioannina na kasar Girika, Nicholas Kantas ya bayyana cewa, yana fatan Beijing za ta gudanar da wasannin Olympics mafi kyau.
A ran nan, aka kawo karshen rana ta biyu ta mika wutar wasannin Olympics na shekarar 2008 a kasar Girika, kuma wutar ta isa birnin Ioannina da ke tsakiyar kasar Girika. A madadin jama'ar lardin Epirus da na birnin Ioannina ne, Nicholas Kantas, magajin birnin, ya sada zumunta a tsakaninsu da jama'ar Sin. Ya ce, "zuciyarmu a hade take da taku, kuma ubangiji ya kiyaye birnin Beijing. Ina fatan Beijing za ta gudanar da wasannin Olympics mafi kyau."(Lubabatu)
|