Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 16:22:09    
Tabbas ne, dukkan makarkashiyar neman lalata harkar mika wutar wasannin Olympic za ta bi ruwa

cri
Yau ranar Laraba, kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya bayar da sharhi cewa, tabbas ne, dukkan makarkashiyar da aka kulla don neman lalala harkar mika wutar wasannin Olympic ba za ta sami nasara ba.

Sharhin ya nuna cewa, harkar mika wutar wasannin Olympic wani biki ne mai girma. Makasudin yadada buri mai daraja na wasannin Olympic da manufofinsa a duniya, shi ne domin nemo wa duk dan adam adalci da zaman lafiya da fahimtar juna da kuma aminci. Amma abin bakin ciki shi ne, yayin da ake yin harkar mika wutar wasannin Olympic na kusan ko wane karo, wasu kungiyoyi da mutane wadanda ke da makirshi su kan tada zaune tsaye da lalata harkar nan, don neman samun martani sosai daga wajen kafofin watsa labaru. Manufarsu kuwa iri daya ce, wato suna neman cim ma burinsu ta ko wace mummunar hanya.

Sharhin ya jaddada cewa, wutar wasannin Olympic mai dauke da burin dukkan 'yan adam tana samun kyakkyawar marhabin daga wajen nagartattun jama'a. Wutar tana haskaka kyakkyawar makomar 'yan adam, kuma tana nuna ainihin wasu kungiyoyi da mutane wadanda suka kulla makarkashiya. Wutar wasannin Olympic tana wakiltar karfin adalci da dukkan 'yan adam ke nunawa ba tare da tsoron kome ba, tabbas ne, dukkan makarkashiyar da aka kulla don neman tada zaune tsaye da shuka barka za ta bi ruwa. (Halilu)