Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 14:40:02    
Bayani dangane da 'yanuwa biyu masu yin zane-zane da suka fito daga wani iyali mai suna Zhou

cri

'Yanuwa biyu da suka fito daga iyali mai suna Zhou su ne shahararrun masu kwarewar fasaha da suka yi suna a kasashen duniya , zane-zanen fenti da mutum mutumin da suka sassaka da zane-zane irin na Engraving da suka yi sun jawo sha'awar mutane sosai.

Daga cikinsu, sunan yaya (wa) shi ne Zhou Shanzuo, sunan kanne shi ne Zhou Dahuang . A farkon shekaru 50 na karnin da ya wuce, , an haife su a jihar kabilar Zhuang mai ikon aiwatar da harkokinta na kanta wadda ta yi suna sosai saboda samun ni'imtattun yankuna da wakokin tsaunuka. A kan manyan jikunan tsaunuka na garinsa, an sami tsofaffin zane-zane na zamani aru aru wadanda suke da tarihi na shekaru fiye da dubu 2, ana kiran irin zane-zane da cewa, "zane-zanen tsaunin Huashan, zaune-zanen da aka yi a kan jikunan tsaunuka na da sifofin mutane da dabbobi da tsuntsaye iri iri da sauransu wadanda suke bayyanuwa sosai . Mr Zhou Dahuang ya waiwayi cewa, a lokacin da muke karami, mahaifinmu ya kai mu zuwa kogin Ming, mun yi zirga-zirgan kwale-kwale mun dudduba zane-zanen da aka yi a zamani aru aru a jikunan manyan tsaunuka, a wancan lokaci, mun yi mamaki sosai da wadannan zane-zane, muna ta'ajibi da su, har ma sun zama abin tunawa gare mu . Sa'anan kuma, muna kama hanyar bin fasahohi iri iri, muna son mu kago abubuwan da ke da tsabi'u namu na kanmu.

Mr Zhou Dahuang ya bayyana cewa, al'adar fasahar gargajiya da ke kasancewa a tsakanin mutanen garinmu ta dace da na "yan adam sosai, kuma ta ba da tasiri mai karfi garemu kuma ta wayewar kanmu sosai.

A farkon shekaru 80 na karnin da ya gabata, wasu zane-zanen da suka yi sun ba da tasiri mai karfi sosai a cikin babban yankin kasar Sin. A shekarar 1986, 'yanuwan biyu sun tsai da wani kuduri cewa, ya kamata su tafi zuwa kasar Amurka don koyon fasahar yin zane-zane ta kasashen yamma. Daga wancan lokaci, Mr Zhou Shanzuo mai shekaru 34 da Mr Zhou Dahuang mai shekaru 29 sun sauka kasar Amurka kuma sun soma koyon fasaharsu.

Wadannan 'yanuwan biyu sun koyi abubuwan da suke bukata , sun yi zane-zanensu a kan zawwati masu fadi sosai, sun zuba fenti mai launi iri iri da yawa a kan wata kusurwar zawwati , sa'annan kuma sun yi zane-zane da babban buroshi a kan zawwati tare da saurarar kide-kide, wadanda suka dudduba yadda suka yi zane-zane da idonsu na kansu ba su iya tsammanin abin da za su yi ba, amma bayan rabin awa ko awo'i biyu , sai ana iya ganin sifofin mutanen da ke motsi da wasu almomi ko wasu tsafe da suka yi, mutanen da suka ganin yadda 'yanuwan biyu suka yi zane-zane sun yi mamaki sosai kan kwarewarsu. Daga shekarar 1994, wadannan 'yanuwan biyu sun nuna fasaharsu ta yin zane-zane a gaban 'yan kallon da ke wurin nuna wasanni.

A watan Satumba na shekarar da muke ciki, an yi nunin zane-zanen da 'yanuwan biyu suka yi a cikin shekaru 30 a gidan nuna kayayyakin fasaha na kasar Sin, sa'anan kuma sun yi zane-zane a gaban 'yan kallo kai tsaye a dakin nuna wasannin kide-kide da wake-wake na tunawa da Mr Sun Yat Seen, wani malam mai suna Nicole Caros ya ba da kyautar kudi ga nunin nan, ya bayyana cewa, na sauko nan daga birnin Chicago, a ganina, zane-zanen da suka yi na da karfi sosai, kuma na da kyau sosai, mutane Chicago dukansu sun yi musu kauna sosai.

Tsabi'un 'yanuwan biyu na da bambanci sosai, kuma suna da bambanci sosai wajen abubuwan da suke kaunar yi. Mataimakin babban jami'in dakin nune-nune na 'yanuwan biyu Mr John Clark ya bayyana cewa, a wani lokaci, Mr Zhou Dahuang ya yi wasu zane-zane, amma da Mr Zhou Shanzuo ya zo ya gani, sai ya goge wasu kashi, sa'anan kuma ya sake yin wasu zane-zane a kai, a ganina, yin hakan na da amfani gare su wajen yin zane-zane.

"Yanuwan biyu sun yi hadin guiwar yin zane-zane har cikin shekaru fiye da 30, dukkan zane-zane su biyu ne suka yi cikin hadin guiwa, Ba a iya zaton cewa, 'yanuwan biyu da ke da bambancin tsabi'u, amma su iya yin zane-zanen da ke halayen musamman na jituwa.

'Yanuwan biyu sun bayyana cewa, tun daga farko, mun yi fatan zane-zanen da muka yi za su nuna halin jituwa da ake ciki, amma a karshe dai, mun fahimci cewa, samun bambanci wajen fasahar yin zane-zane, abu ne da ya faru a yau da kullum, irin wannan sabanin da ke tsakanimu zai kawo mana sakamakon da ba mu taba samuwa ba.Yanzu, wasu masu manyan kamfanoni sun tanada zane-zanen 'yanuwan biyu da yawa, wasu 'yan siyasa masu fasaha su ma suna kishin zane-zanensu. (Halima)