Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 14:37:58    
Beijing ta kaddamar da muhimman harkokin al'adu na wasannin Olympic

cri
Ran 20 ga wata da dare, kungiyar wasannin kwaikwayon wake-wake ta kasar Sin ta nuna manyan wasannin kwaikwayo a dakin kide-kide na birnin Beijing. Wannan ya alamantar da cewa, Beijing ta kaddamar da muhimman harkokin al'adu na wasannin Olympic na tsawon rabin shekara a hukunce.

Beijing za ta yi gasar wasannin Olympic a watan Agusta na wannan shekara. Gasar wasannin Olympic da za a yi a wannan karo ba kawai wata gasa ba ce, ita ce kuma wani dandamali, inda yankuna da kabilu daban daban na duk duniya za su yi mu'amalar al'adu. Bisa shirin da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da ma'aikatar al'adu ta kasar Sin suka tsara, an ce, tun daga ran 20 ga watan Maris zuwa karshen watan Satumba na wannan shekara, daya bayan daya za a nuna nagartattun wasannin kwaikwayo fiye da iri 140 kuma sau dari 6 a nan Beijing, wadanda za su hada da wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da wasannin kwaikwayo na waka na zamanin yau da kide-kiden symphony da shagulgulan kide-kide da raye-raye da kide-kiden kabulu na kasar Sin da wasan taka-juye da dai sauransu.

A lokacin da yake zantawa da wakilinmu, Liu Zhongjun, mataimakin darektan sashen fasaha na ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ya yi karin bayanin cewa, harkokin al'adu na wasannin Olympic da ake yi a Beijing sun fi yawa, kuma sun hada da ire-iren fasaha kan dandamali mafiya yawa a kasar Sin tun bayan shekaru 1950 har zuwa yanzu. Ya kuma kara da cewa, dukkan wasannin kwaikwayo da za a nuna a wannan karo sun fi shahara a duniya, amma farashin tikitoci na da rahusa. Ya ce,'Mun zabi wadannan wasannin kwaikwayo daga duk kasar Sin. Baya ga wasu nagartattun wasannin kwaikwayo da aka nuna a shekarun baya, za a nuna wasu shahararru da kuma wasu wasannin kwaikwayo na gargajiya. Sa'an nan kuma, a muhimmiyar ranar da ya rage kwanaki 100 da kuma kwanaki 50 da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing, za a nuna wasu wasannin kwaikwayo na musamman. Wadannan wasannin kwaikwayo za su kawo wa gasar wasannin Olympic murna, za su kuma kawo wa 'yan kallo damar kara fahimta kan fasaha. Bugu da kari kuma, galibin tikitoci na da rahusa, gwamnatin Sin za ta ba da taimako. Ta biya kudaden yi hayar dakunan wasannin kwaikwayo, ta kuma ba da kudaden alawas ga kungiyoyin wasannin kwaikwayo, ta haka ta tababtar da ganin cewa, 'yan kallo za su shiga dakunan wasannin kwaikwayo domin jin dadin kallon wasannin kwaikwayo da tikitoci mafiya rahusa.'

Mr. Liu ya kara da cewa, in an kwatanta su da sauran wasannin kwaikwayo da aka nuna domin cin riba, farashin tikitocin da za a sayar a wannan karo ya ragu da rabi. Bugu da kari kuma, masu shirya harkokin za su bai wa rukunonin musamman, kamar su 'yan makarantu gatanci wajen sayen tikitoci.

Lu Kaiwang, mai kula da harkokin sayar da tikitocin kallon muhimman harkokin al'adu na wasannin Olympic ya kyautata fatan kan yawan 'yan kallon da za su kallo wadannan harkoki. Ya gaya mana cewa,'Tun daga yanzu har zuwa karshen watan Satumba, za a nuna wasannin kwaikwayo fiye da 600, wato ke nan za a nuna wasu fiye da 100 a ko wace wata. A lokacin gasar wasannin Olympic, za a nuna wasannin kwaikwayo da dama masu ban sha'awa a ko wace rana. A lokacin, Beijing za ta maraba da baki daga ko ina a duniya, wadanda suka hada da 'yan wasa da masu yawon shakatawa na kasashe daban daban. Za su kalli wasannin kwaikwayo iri daban daban, ina tsammani cewa, za su ji dadin kallonsu.'

Game da batutuwa da dama da wasu suka nuna damuwa a kai, kamar wasu 'yan kallo ba su san ka'idojin kallon wasannin kwaikwayo sosai ba, Mr. Lu yana ganin cewa, za a nuna dukkan wadannan wasannin kwaikwayo a dakunan wasannin kwaikwayo, shi ya sa za a bukaci 'yan kallo masu inganci da suka lakanci ka'idojin kallon wasannin kwaikwayo sosai. Amma duk da haka, a shekarun baya, ta hanyoyi daban daban ne Beijing ta yi ta jagorantar 'yan kallo da su mai da hankulansu kan wayin kai da ladabi, shi ya sa an yi imani da cewa, kyawawan halayen da 'yan kallo za su nuna za su sami gamsuwa daga 'yan wasannin kwaikwayo da kuma ma'aikata masu aikin wasannin kwaikwayo.

Wata sabuwa kuma, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta kuma gayyaci dimbin mashahurran kungiyoyin fasaha na ketare da su zo Beijing domin gama kansu da takwarorinsu na kasar Sin wajen nuna wa mutanen Sin da na waje wasannin kwaikwayo mafiya ban sha'awa a jajibirin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Kazalika kuma, wasu dakunan ajiye kayayyakin tarihi da dakunan nune-nunen kayayyakin fasaha sun riga sun fara shirya nune-nune iri daban daban domin neman yin kokarinsu wajen nuna al'adun gargajiya da kuma fasahar zamanin yau na kasar Sin.