Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 12:41:20    
Rukunin Dalai Lama ya ta da tarzoma a Lhasa domin kawo wa kasar Sin baraka, in ji masanin ilmin Tibet

cri
Ran 26 ga wata, a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, Sonam Doji, manazarci na cibiyar nazarin ilmin Tibet ta kasar Sin kuma masani mai ilmin Tibet ya bayyana cewa, tashe-tashen hankulan da suka faru a birnin Lhasa da wasu sauran yankunan kabilar Tibet a kwanan baya ba batun addini ba ne, su laifuffuka ne da rukunin Dalai Lama ya yi bisa fakama da addini domin lalata dinkuwar kasar Sin da kuma hada kan al'umma.

Sonam Doji ya kara da cewa, bayan 'yantar da jihar Tibet cikin lumana a shekarar 1951, an kubutar da 'yan Tibet daga mawuyacin hali da kuma mugun tsarin bauta na gargajiya, kuma rukunin Dalai Lama bai iya ci gaba da ci da gumin 'yan Tibet ba. Dukkan tarzomar da rukunin Dalai Lama ya tayar tare da makamai a shekarar 1959 da kuma tashe-tashen hankula da suka wakana a wannan karo a Lhasa da sauran yankunan kabilar Tibet, munanan aikace-aikace ne da rukunin Dalai Lama ya yi domin neman ci gaba da samun riba da kuma maido da mulkinsa.

Game da kalamin da rukunin Dalai Lama ya baza a ketare, wato wai 'yan Tibet ba su da 'yancin bin addini, Sonam Doji ya ce, bisa ka'idojin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Sin, an ce, kasar Sin tana aiwatar da manufar bin addini cikin 'yancin kai. Ana gudanar da wannan manufa a jihar Tibet yadda ya kamata. Yanzu akwai gidajen ibada manya da kanana da kuma wuraren yin harkokin addini guda 1787 a jihar Tibet, ta haka dukkan masu bin addini sun iya yin harkokin addini yadda ya kamata.(Tasallah)