Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 12:20:10    
Rana ta biyu ta mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing a kasar Girka

cri

Ran 25 ga wata, an kammala aiki na rana ta biyu da aka mika wutar yola ta gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008 a kasar Girka.

A wannan rana, a daidai karfe 9 da safe ne wutar yolar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta fara zuwa arewa daga birnin Mesologi da ke tsakiyar Girka. Bayan da ta ratsa biranen Agrinion da Amfilokhia da Arta, a karshe dai ta isa birnin Janina a ran nan misalin da karfe 6 da minti 30 da yamma, inda wutar yolar ta yada zango a wurin.

Birnin Janina, babban birni ne na lardin Epirus da ke tsakiyar Girka. An yi kasaitaccen biki a babban filin da ke cibiyar birnin domin maraba da wutar yolar. Ran 25 ga wata, rana ce ta cika shekaru 187 da kafuwar kasar Girka. Mazauna wurin sun sanya tufafi irin na kabilarsu, sun yi wake-wake da raye-raye domin murnar ranar cika shekaru 187 da kafuwar kasarsu da kuma harkar mika wutar yolar.

Daga baya kuma, za a ci gaba da mika wutar yola a Girka har na tsawon sati guda. Wutar yolar za ta isa birnin Athens, hedkwatar Girka a ran 30 ga wata, inda za a mika wa birnin Beijing wutar yolar.(Tasallah)