Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 11:41:30    
Rogge ya nuna yabo kan manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a shekarun baya

cri

Ran 24 ga wata, a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar L'equepe ta kasar Faransa a birnin Olympia na kasar Girka, Jacques Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya bayyana cewa, a shekarun baya, kasar Sin ta sami babban ci gaba a fannoni daban daban. Bayan da birnin Beijing ta sami damar daukar bakuncin gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, kasar Sin ta sami kyakkyawar bunkasuwa a fannin tinkarar gurbata muhalli da dai sauransu.

Wannan shugaba ya kara da cewa, kasar Sin ta sami babban ci gaba. In wani ya kai wa kasar Sin ziyara, to, zai gane irin wannan ci gaba.

Ya kuma jaddada cewa, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ba wata kungiyar siyasa ba ce, haka kuma, ba wata kungiyar aikin soja ba ce, nauyinsa shi ne shirya nagartacciyar gasar wasannin Olympic domin dukkan 'yan wasa. Tilas ne 'yan wasa da ke shiga gasar wasannin Olympic su bi ka'idojin da ke cikin 'kundin tsarin wasannin Olympic'.(Tasallah)