Ran 25 ga wata, wakilinmu ya ruwaito mana labarin cewa, hukumar tabbatar da tsaron al'umma ta birnin Lhasa ta yi karin bayani da cewa, ya zuwa yanzu mutane 280 ko fiye da ake zarginsu da ta da mummunar tarzoma a Lhasa sun ba da kansu ga hukumar.
A cikin wadannan mutane, wasu sun ta da tarzomar domin tsirarun masu laifi sun zuga su ne, wasu kuma masu laifi ne suka tilasta musu, wasu kuwa 'yan a-ware masu neman samun 'yancin kan Tibet ne suka yi hayarsu da kudade.
Saboda wasu daga cikin wadannan mutane fiye da 280 ba su yi munanan laifuffuka ba, kuma sun ba da kai da kansu, shi ya sa a kwanan baya, hukumar tabbatar da tsaron al'umma ta Lhasa ta saki wasu daga cikinsu.
Ban da wannan kuma, hukumar gabatar da kararraki ta Lhasa ta ba da iznin kama mutane 29 da ake tuhumarsu da laifin kawo wa tsaron kan kasar Sin barazana da kuma mugun laifi. Hukumomin aiwatar da dokoki na Lhasa sun bayyana cewa, za su yanke hukunci kan munanan masu laifuffuka bisa abubuwan gaskiya da kuma dokoki.(Tasallah)
|