Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-26 11:16:59    
Manema labaru na Sin na fatan takwarorinsu na yammacin duniya kada su sa gishiri a labaru kan tashin hankali a Lhasa

cri
A kwanan baya, ta hanyoyi daban daban wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya sun bayar da labaru tare da sa gishiri a ciki kan tashe-tashen hankulan da suka faru a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kanta ta kasar Sin a ran 14 ga wata. Game da wannan, Zhai Huisheng, mai kula da hadaddiyar kungiyar manema labaru ta kasar Sin ya bayyana cewa, yana fatan kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya za su girmama ainihin abubuwa yadda ya kamata, kada su ci gaba da watsa labarun marasa gaskiya.

Mr. Zhai ya kara da cewa, labaru masu yawa da kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya suka bayar kan tashe-tashen hankula a Lhasa sun saba wa ka'idojin da ake bi wajen watsa labaru, wato girmama abubuwan gaskiya da kuma watsa labaru kan abubuwa yadda suke kasance. Sa'an nan kuma, ko da yake muhimman kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya sun ba da labaru kan ra'ayin gwamnatin kasar Sin, amma sun fi tsamo karin kalami daga bakin rukunin Dalai Lama, sun fi bayyana ra'ayinsa.

Mr. Zhai ya ci gaba da cewa, in aka ba da labaru marasa gindi, to, za a keta ka'idoji mafiya muhimmanci a fannin yada labaru, haka kuma, za a raunana mutuncin kafofin yada labaru sosai.(Tasallah)