Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 20:36:23    
Tawagar ba da hidima ta yanayi ta mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta fara tattaruwa zuwa dutsen Everest

cri

A ran 25 ga wata, shugaban karamar kungiyar ba da hidima kai tsaye ta tawagar ba da hidima ta yanayi ta mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics ta Beijing Mr Yang Xingguo ya bayyana cewa, mambobin tawagar sun fara tattaruwa zuwa birnin Lhasa, domin gudanar da aikin tabbatar da yanayi kafin lokacin da za a kai wa juna wutar yola a dutsen Everest.

A 'yan kwanakin baya, Mr Yang yana aiki yana yin shirin hawan dutsen Everest. A ran 27 ga wata, sauran mambobi za su isa birnin Lhasa ta jiragen sama. A ran 28 ga wata, dukkan mambobin tawagar ba da hidima za su tattaru a birnin Lhasa, sa'an nan kuma, za su tashi zuwa babban sansani da ke kan dutsen Everest mai tsawon mita 5200. Za a shafe wata daya zuwa biyu domin wannan aikin ba da hidima.

Mr Yang ya ce, an riga an tabbatar da hanyar da za a bi domin hawa dutsen Everest da wutar yola, amma ba a tsaida lokacin ba tukuna. Babban aiki na tawagarsa shi ne, tabbatar da yanayi na gaskiya, domin a tsaida lokacin hawa kolin dutsen Everest da wutar yola.(Danladi)