Yau ranar Talata, kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya bayar da sharhi cewa, neman lalata wasannin Olympic da rukunin Dalai Lama ke yi ya saba wa burin jama'a.
Sharhin ya ce, yanzu, jama'ar kabilu daban daban na kasar Sin suna kazar-kazar wajen shirya wasannin Olympic na Beijing. Amma rukunin Dalai Lama ya dauki wasannin Olympic na Beijing bisa matsayin wata kyakkyawar damar da ba safai ya iya samu ba don mayar da harkar neman "yancin kan Tibet" da ta zama ta kasa da kasa. Dalai Lama ya sha yin sanarwa a shekarar bara cewa, "shekarar 2008 wata muhimmiyar shekara ce, watakila 'yan Tibet za su sami damar karshe daga wajen wasannin Olympic." Yayin da yake karbar ziyarar da manema labaru suka yi masa a watan Janairu da ya wuce, ya kara neman mabiya da magoya bayansa su yi zanga-zanga a lokacin wasannin Olympic na Beijing, don yin farfaganda a kan abu na wai "yancin kan Tibet."
Kungiyar samari ta Tibet wadda ita ce kungiya mafi girma ta rukunin Dalai Lama ta gabatar da ra'ayinta cewa, za su yi aikace-aikacen neman 'yancin kan Tibet ta hanyar ta'addanci.
Bayan haka sharhin ya kara da cewa, sanin kowane, babu kasa ko daya a duniya ke ganin shaidar 'yancin kan Tibet, kuma babu gwamnatin kasa ko daya ke amince da wai "gwamnatin gudun hijira" ta Dalai. Tabbas ne, makarkashiyar da rukunin Dalai Lama ya kulla don yin amfani da wasannin Olympic na Beijing wajen kawo wa duniya tasirinsa na jawo wa kasar Sin baraka za ta bi ruwa. (Halilu)
|