Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 16:43:50    
Wasannin Olympic na Beijing yana samar da babbar dama ta fuskar kasuwanci

cri
Bayan da aka fara bikin mika yola ta wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008, an soma yin harkokin wasannin Olympic na Beijing. Sa'an nan wasannin Olympic na Beijing yana samar da babbar dama ta fuskar kasuwanci. Yanzu, akwai kamfanoni 63 wadanda suka ba da kudin taimako ga wasannin Olympic na Beijing. Mr Heiberg, shugaban kwamitin raya kasuwanci na hukumar wasannin Olympic ta duiya ya bayyana ra'ayinsa cewa, bisa yawan kamfanonin nan da yawan kudin taimakon da suka bayar, wasannin Olympic na Beijing zai zama wani taron wasannin Olympic da za a sami kudi mafi yawa daga wajensa, ko kuma zai zama wani taron wasannin Olympic da za a shirya tare da samun kyakkyawar nasarar da ba a taba samu irinta ba a da.

Kamfanoni da yawa wadanda suka ba da taimakon kudi suna amfani da babbar dama da suke samu daga wajen wasannin Olympic na Beijing don kara samun bunkasuwa. Mr Yuan Bin, ministan raya kasuwanni na kwamitin kula da shirya wasannin Olympic na Beijing ya bayyana cewa, ta hanyar bunkasa tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri sosai, an kara azurta samfurin Olympic. (Halilu)