Magangarar ruwa mai suna Huangguoshu tana lardin Guizhou da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. Wannan magangarar ruwa ita ne mafi girma a kasar Sin. Tsayin magangarar ruwan nan ya kai mita 74, wato ke nan ya tashi daidaita da tsayin wani gini mai hawa sama da 20. Ruwa na fadowa da sauri daga kokuwar kwazazzabai zuwa kwari mai zurfi, in ka gani, sai ka ce, lallai, fadowar ruwan nan ta yi kamar manyan rakuman ruwa da ke tashi da sauka a cikin koguna. Karar da ake ji a yayin da ruwan ke cin karo da duwatsu ta yi amo sosai, kana kuma wani abu kamar hazo kan tashi sama-sama. In wani ya tsaya a wuri mai nisan mita 50 ko 60 daga magangarar ruwan nan, to, tufafinsa za su jika shakwab da ruwa da ke fitowa daga magangarar ruwan nan.
1 2 3
|