Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-25 15:39:04    
Aikin fassara da Larabci ya zama wata muhimmiyar hanya wajen tura manoma zuwa waje don ci rani a jihar Ningxia

cri

Gundumar Tongxin da ke tsakiyar jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin wata gunduma ce da ake iya samun dimbin 'Yan kabilar Hui da ke bin addinin Musulunci. Har kullum fararen hula na kabilar Hui suna da al'adar koyon karatun Alkur'ani mai girma da kuma harshen Larabci. Tare da ingantuwar cudanyar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa, ana ta bukatar mutane da suka iya harshen Larabci, sabo da haka aikin fassara da Larabci ya zama wata sabuwar hanya ce ga dimbin 'yan ci rani ta kabilar Hui. Yang Hong, shugaban hukumar kula da ayyukan samun guraban aikin yi ta gundumar Tongxin ya bayyana cewa,

"A 'yan shekarun nan da suka gabata, tare da bunkasuwar cinikayya tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata, kasuwannin lardunan Zhejiang da Guangdong da Fujian da dai sauransu na kasar Sin suna jawo hankulan 'yan kasuwa Larabawa kusan dubu 300 a ko wace shekara. Sabo da haka manoma masu aikin fassara da Larabci na gundumarmu sun samu wata hanya wajen samun wadata."

Ya zuwa yanzu, yawan masu aikin fassara da Larabci yan asalin gundumar Tongxin da ke birnin Yiwu na lardin Zhejiang da birnin Guangzhou na lardin Guangdong ya riga ya kai 875, kuma mutane 26 suna gudanar da aikin fassara a kasashen Larabawa na shiyyar gabas ta tsakiya. Ta haka aikin fassara da Larabci ya riga ya zama wata muhimmiyar hanya ce wajen tura manoma 'yan kabilar Hui zuwa waje don ci rani.

Tian Shuhai, wani manomi ne na gundumar Haiyuan da ke kudancin jihar Ningxia, inda ake fama da talauci sosai. Ya gama karatunsa daga makarantar koyar da harshen Larabci ta gundumar Tongxin na jihar Ningxia a shekara ta 2003, yanzu yana gudanar da aikin fassara da Larabci a birnin Guangdong. Kuma ya gaya mana cewa, yana iya samun kudaden Sin yuan 5000 a ko wane wata. Ya kara da cewa,

"Ni ne mutumin farko daga kauyenmu wajen koyon harshen Larabci. Ganin wadatar da na samu, yanzu mutane 8 na kauyenmu sun riga sun fara koyon harshen. Idan na samu isasshen kudi, zan bude wani kamfanin ciniki, ta yadda zan iya ba da taimako ga iyalaina da abokaina masu aikin fassara da Larabci."

Domin ci gaba da raya aikin tura masu fassara da Larabci zuwa waje, gundumar Tongxi ta sa kaimi ga bunkasa hukumomin horar da masu aikin fassara da Larabci. Kuma ya zuwa yanzu an riga an kafa makarantun koyar da harshen Larabci 7, inda yawan malamai masu koyar da harshen ya zarce dari, kuma yawan daliban da ke shiga kwas din horaswa ya kai fiye da 1000 a ko wace shekara. Shugaban makarantar koyar da harshen Larabci na gundumar Tongxi na jihar Ningxxia Bai Shengyun ya bayyana cewa,

"Aikin horar da masu aikin fassara da Larabci yana da ma'ana sosai, a fannin siyasa, ta kara ingantuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Larabawa, kuma a fannin tattalin arziki, ba kawai masu aikin fassara da Larabci sun samu dimbin kudade ba, har ma sauran mutane sun samu wannan hanyar samun kudi ta tallafawar da suka bayar."(Kande Gao)